Dattawan Zamfara sun zargi hukumomin tsaro da sakin 'yan bindigan da suka kama

Dattawan Zamfara sun zargi hukumomin tsaro da sakin 'yan bindigan da suka kama

  • Kungiyar dattawan jihar Zamfara ta koka da yadda jami'an tsaro ke sakin 'yan ta'adda bayan sun kama su ko kuma wadanda aka mika musu
  • Tsohon Sanata, Saidu Dansadau, ya ce wannan ya na daga cikin dalilin da yasa ta'addanci ya ki ci balle cinyewa a jihar
  • Ya jinjina wa kungiyoyin da suke kafa gidauniya a yankin domin tallafawa marayun yara da suka rasa iyayensu sakamakon ta'addanci

Gusau, Zamfara - Wata kungiyar dattawan jihar Zamfara ta koka kan zargin da ta ke na cewa jami'an tsaron jihar suna sakin 'yan bindigan da suka kama.

Kungiyar ta yi kira ga hukumomi da su daina hakan inda ta kafa wannan a matsayin dalilin da ke karo hauhawar rashin tsaro a jihar.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron da ta yi a Gusau, babban birnin jihar yayin da ta ke bayyana mummunan halin da yara marayu suke ciki sakamakon ta'addancin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

Tsohon sanata, Saidu Dansadau, ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron, Premium Times ta ruwaito.

Dattawan Zamfara sun zargi hukumomin tsaro da sakin 'yan bindigan da suka kama
Dattawan Zamfara sun zargi hukumomin tsaro da sakin 'yan bindigan da suka kama. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kwamitin ya nuna fushinsa kan yadda hukumomi ke sakin 'yan ta'adda da aka kama ko kuma wadanda sojoji, 'yan banga ko wasu hukumomin tsaro suka mika musu," yace.
"Muna kira ga hukumomin tsaro a jihar nan saboda Allah da su kiyayi sakin 'yan ta'adda kuma su dinga gurfanar da su domin sakinsu ya na daya daga cikin dalilin da ke kawo hauhawar ta'addanci a jihar."

Ya ce kungiyar ta jinjinawa kungiyoyin yankin da ke samar da gidauniyar tallafin karatun firamare da sakandare domin yaran da iyayensu suka rasa rayukansu sakamakon ta'addanci a jihar.

Dansadau ya ce tabbas lamarin tsaron jihar ya kara inganta daga yadda aka datse layikan sadarwa a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

Ya ce, wurare kamar kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi suna cikin wuraren da 'yan ta'addan yanzu ke kai farmaki.

Zamfara: Hayar bindiga muke yi domin sheke mutane da satar shanu, 'Yan bindiga 3

Hukumar NSCDC ta tabbatar da damke wasu mutum uku da ake zargin 'yan bindiga ne yayin da suka tsere zuwa yankin Magami da ke Zamfara sakamakon ruwan wuta da sojoji ke musu.

Ikor Oche, kakakin hukumar NSCDC, ya tabbatar da wannan cigaban a taron manema labarai inda yace wadanda aka kaman sun shiga hannu ne yayin da suke tashar mota da ke Gusau a ranar Litinin.

Oche ya ce an kama wadanda ake zargin da safe yayin da suke kokarin shiga mota zuwa Taraba domin haduwa da sauran miyagun da suka koma can, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel