Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sojojin da ke bakin daga da su dage saboda ana matakin karshe na yaki da ta'addanci
  • Buhari wanda ya yi jawabi ga dakarun, ya ce 'yan Najeriya na mika godiyarsu da yabawarsu kan sadaukarwar da sojojin suke yi
  • Ya yaba da yadda zaman lafiya ya dawo arewa maso gabas kuma ya na fatan lamurran tattalin arziki su dawo kamar yadda suke a da

Borno - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga dakarun sojin rundunar Operation Hadin Kai da su cigaba da kokari yayin da suke shiga matakin karshe na yaki da ta'addanci.

Kamar yadda sanarwar da Femi Adesina ya fitar, Buhari ya sanar da hakan a ranar Alhamis a sansanin sojin sama da ke Maiduguri, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda
Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

TheCable ta ruwaito yadda mayakan ta'addancin ISWAP suka harba roka a Maiduguri kafin ziyarar Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

A yayin jawabi ga dakarun, Buhari ya ce dukkan kasar nan tana godiya kan kokarin da suke nunawa wurin dawo da zaman lafiya ga yankin arewa maso gabas, yayin da ya ke jajanta wa iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu ko suka samu rauni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasan ya ce gwamnati za ta cigaba da tabbatar da cewa mata da yaran sojojin da suka rasu an cigaba da taimaka musu.

"Babu aikin da ya kai naku saboda kun san irin bukata da dagewar da ake so ku yi saboda sauran jama'a," Buhari yace.
"Bari in fara da jajanta muku kan mutuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkushu da sauran jami'an birged na 25 da 28 wadanda suka rasu a ranar 13 ga watan Nuwamban 2021.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

"Na san cewa mun rasa wasu a wasu sassan kasar nan yayin da suke kan aiki.
"Jama'ar jihar Borno da dukkan kasar nan suna mika muku godiya kan yadda kuke sadaukar da rayukan ku domin samar da zaman lafiya.
"Ina kira gare ku da ku mayar da hankali wurin kawo karshen dukkan ta'addanci tare da dawo da al'amuran tattalin arziki a arewa maso gabas da sauran sassan kasar nan inda 'yan Najeriya ke da damar al'amuran rayuwarsu ba tare da tsoro ko hantara ba," shugaban kasan ya kara da cewa.

Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin sama da ke yankin Ngomari a Maiduguri yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin sauka a birnin yau Alhamis.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, daya da cikin makaman masu linzami ya tsallake har zuwa Ajilari, kusa da filin jiragen sama na Maiduguri inda sansanin sojoji ya ke.

Kara karanta wannan

Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno

Majiyoyi sun ce mutum daya ya rasa ransa a Ngomari yayin da wasu suka samu raunika a yankin Ajilari. Alamu suna nuna cewa, maharan sun daidaita tare da saitar filin saukar jiragen saman ne saboda makaman sun sauka 10:45 na safe, mintoci kadan kafin isar Buhari birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel