Kano: 'Yan sanda sun yi ram mutum 3 masu safarar miyagun kwayoyi da dillancinsu

Kano: 'Yan sanda sun yi ram mutum 3 masu safarar miyagun kwayoyi da dillancinsu

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 3 bisa zarginsu da safarar miyagun kwayoyi daga Onitsha
  • Ana zargin sune masu kai wa ‘yan daban jihar kayan maye kuma matasa ne ‘yan asalin jihar Katsina masu karancin shekaru
  • An kama su ne miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol, Exol da Diazepam tare wasu kudade

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi ram da wasu matasa uku bisa zarginsu da safarar miyagun kwayoyi cikin jihar Kano ga ‘yan daba.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta kakakinta, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wadanda ake zargin sun hada da Rabiu Idris mai shekaru 22, Abdullahi Muhammad mai shekaru 20 da Sunusi Sani mai shekaru 23 wadanda duk ‘yan asalin jihar Katsina ne daga karamar hukumar Safana.

Kano: 'Yan sanda sun yi ram mutum 3 masu safarar miyagun kwayoyi da dillancinsu
Kano: 'Yan sanda sun yi ram mutum 3 masu safarar miyagun kwayoyi da dillancinsu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, cikin miyagun kwayoyin da aka kama su da su sun hada da Tramadol, Exol da Diazepam, inda ya kara da cewa an samu N150,600 daga hannunsu, wanda akwai ‘yan N50, N500 da ‘yan N1000 wadanda duk cinikin kwayoyin ne.

“A ranar 20 ga watan Oktoban 2021 mu ka samu rahoto akan wata kungiyar masu safarar kwayoyi ga ‘yan daba tare da wasu masu laifukan a cikin birnin Kano.
“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Samaila Shuaibu Dikko, ya bayar da umarni ga wata runduna wacce SP Buba Yusuf ya jagoranta akan su kamo wadanda ake zargin.
“Bayan yin wasu bincike mun gano cewa tun daga Onitsha su ke siyo kayan mayen su yi musu kudin mota har jihar Kano. Da bakinsu sun sanar da yadda su ka zo Kano tun daga jihar Katsina saboda sana’ar,” a cewarsa.

Zamfara: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a maboyarsu, sun samo shanu da miyagun makamai

A wani labari na daban, jami'an 'yan sandan jihar Zamfara sun samo bindigogi takwas bayan kai samame wata maboyar 'yan bindiga da ke kusa da Bayan Ruwa a karamar hukumar Maradun ta jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce jami'ai na musamman ne suka kai samamen bayan samun bayanan sirri, Daily Trust ta ruwaito.

"Jami'an sun yi arangama da 'yan daban inda suka kashe da yawa daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.
“A yayin binciken wurin, an samo bindigogi takwas kirar AK47, bindigar harbo jirgin sama da alburusai masu tarin yawa," ya kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel