Halin da hadiman shugaba Buhari ke ciki bayan kamuwa da cutar COVID19, Fadar shugaban kasa ta magantu

Halin da hadiman shugaba Buhari ke ciki bayan kamuwa da cutar COVID19, Fadar shugaban kasa ta magantu

  • Fadar shugaban ƙasa tace babu wani canjin lafiya a tattare da hadiman shugaba Buhari da aka tabbatar sun kamu da korona
  • Femi Adeshin yace waɗan da ke kusa da Buhari mutane ne kamar kowa, duk wani abu da zai iya shafar mutane zai iya faɗawa kan su
  • Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, na ɗaya daga cikin waɗan da abun ya shafa, amma yace yana cikin koshin lafiya

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa babu wani sabon canji tattare da lafiyar hadiman Buhari bayan gano suna ɗauke da cutar COVID19, "Kuma a halin yanzun sun killace kan su."

Mai baiwa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan yaɗa labarai, Femi Adeshina, shine ya bayyana haka a shirin 'Sunday Politics' na Channels tv.

Yace wannan abun da ya faru, "ya kara tabbatar da cewa hadiman shugaban ƙasa mutane ne ba su fi karfin abin da ke faruwa ba."

Kara karanta wannan

Bayan Hadiman Shugaban kasa sun kamu da COVID-19, an bayyana halin da Buhari ke ciki

Femi Adesina
Halin da hadiman shugaba Buhari ke ciki bayan kamuwa da cutar COVID19, Fadar shugaban kasa ta magantu Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Jawabin Adeshina shine na farko da ya tabbatar da cewa cutar Korona ta shiga fadar shugaban ƙasa, kamar yada majiyoyi suka shaida wa Premium Times.

Amma gwamnatin tarayya ta yi gum da bakin ta kan faruwar lamarin har sai da labarin ya fito kuma ya watsu.

Majiya ta bayyana sunayen waɗan da cutar da kama sun haɗa da; Dogarin shugaban ƙasa, ADC Yusuf Dodo, shugaban tsaro, CSO Aliyu Musa, da kuma kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu.

Wata majiya ta haɗa da ministan yaɗa labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, amma daga baya ministan ya bayyana cewa ba abin da ya same shi.

Garba Shehu ya tabbatar da kamuwarsa

Garba Shehu, wanda ya tabbatar wa manema labarai cewa ya kamu da COVID19, yace ba shi da tabbacin wasu hadiman Buhari sun harbu da cutar.

Kara karanta wannan

Wasikar Sulhu: Gwamna Masari ya maida zazzafan Martani ga kasurgumin dan bindiga, Bello Turji

Shehu ya ƙara da cewa ya samu koshin lafiya, kuma ya yi ikirarin cewa bai jima da kammala motsa jiki ba, amma wajibi sai ya samu shaida daga likitoci cewa ya warke daga cutar.

Yace:

"Ba ni da tabbacin waɗan nan mutanen da kuka ambata sun harbu, amma tabbas na kamu da wani nau'in COVID19. Tun da farko ban ji komai ba, kila saboda na yi rigakafi har sau uku."
"A yanzu da nake magana da ku, ina jina cikin koshin lafiya 100% domin yanzu na gama gudun motsa jiki na awa ɗaya."
"Amma bakon abin da wannan rashin lafiya ya zo da shi shine, likitoci ne kaɗai za su tabbatar da mutum ya warke, amma a yanzun ina bin dokoki, na killace kaina."

Hadiman Buhari mutane ne kamar kowa - Adesina

Yayin da Adesina ke martani kan labarin, yace waɗan da ke tare da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, mutane ne kamar kowa, za su iya kamuwa da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

"Duk abin da zai iya faruwa da mutane, zai faru da hadiman shugaban ƙasa. Matsayin da muka taka bai sa mun fi ƙarfin wasu abubuwa su faru da mu ba."

A wani labarin na daban kuma Minista yace nan gaba da kaɗan yan Najeriya za su dora wa Buhari laifi idan ba su samu juna biyu ba

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi , ya roki yan Najeriya su daina ɗora wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, laifin duk kalubalen da suke fuskanta a ƙasa.

Ministan ya yi ikirarin cewa nan gaba za'a iya samun mutanen da za su zargi Buhari matukar ba su samu juna biyu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel