Wasu yan Najeriya za su zargi Buhari idan ba su samu haihuwa ba, Minista

Wasu yan Najeriya za su zargi Buhari idan ba su samu haihuwa ba, Minista

  • Ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya koka kan yadda yan Najeriya ke ɗora wa Buhari kowane laifi
  • Ministan ya yi ikirarin cewa nan gaba za'a iya samun mutanen da za su zargi Buhari matukar ba su samu juna biyu ba
  • Yace gwamnatin shugaba Buhari ta inganta hanyoyin samun kudin shiga, wanda ya farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa

Abuja - Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya roki yan Najeriya su daina ɗora wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, laifin duk kalubalen da suke fuskanta a ƙasa.

Amaechi, wanda tsohon shugaban ƙungiyar gwamnoni ne, ya yi wannan furucin yayin wata hira da Channels TV mai taken, "Hard Copy."

Minsitan ya yi ikirarin cewa mutane suna zargin shugaban ƙasa Buhari da abin da bai shafe shi ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

Rotimi Amaechi
Wasu yan Najeriya za su zargi Buhari idan ba su samu haihuwa ba, Minista Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tsohon gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Komai muka ɗakko sai mu dora wa gwamnati, yadda kasan nan gaba idan mutane ba su samu juna biyu ba, za su ce laifin Buhari ne."

Ministan ya ƙara da cewa shugaba Buhari ya samu ƙasar nan ba yadda yake tsammaninta ba, kuma yana iyakacin bakin kokarinsa.

Da aka tambaye shi ko mai yasa Buhari ya gaza saita komai a Najeriya kamar yadda ya yi alƙawari ga shi har ya shafe kusan shekara 7, Amaechi yace ba komai ne za'a samu yadda ake so ba.

Buhari ne ya farfaɗo da tattalin arziki - Amaechi

A cewar ministan gwamnatin shugaban kasa Buhari ta bullo da hanyoyin samun kudin shiga a gwamnatance, ba ta dogara da hanya ɗaya ba.

Amaechi ya kara da cewa wannan gwamnatin ta farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa kuma ta dakatar da shigo da shinkafar kasashen waje.

Shin ana tattauna matsalar tsaro a taron FEC?

Yace matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Najeriya, ba zai yuwu a magance ta ba har sai gwamnati ta kawar talauci a karon farko.

Kazalika Mista Amaechi ya bayyana cewa ba'a tattauna matsalar tsaro a taron majalisar zartarwa na mako-mako.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan zuwansa Legas da rashin zuwa jaje Sokoto

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kare kansa daga sukar da yake sha bayan zuwa Legas a lokacin da aka kashe mutane a Sokoto.

Malam Garba Shehu, yace ba kaddamar da littafi ya kai Buhari Legas ba, ainihin makasudin zuwansa dan jiragen ruwan sojoji ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel