Kano: Bayan zanga-zangan 'yan kasuwa, kotu ta hana Ganduje gina shaguna a Wambai

Kano: Bayan zanga-zangan 'yan kasuwa, kotu ta hana Ganduje gina shaguna a Wambai

  • Babbar kotu mai zama a Kano ta dakatar da gwamnatin jihar daga yin gini a wata hanya da ke kasuwar Kofar Wambai a cikin karamar hukumar Municipal da ke jihar
  • An samu rahotanni akan yadda ‘yan kasuwa su ka dinga zanga-zanga akan ginin shagunan bayan gwamnatin jihar ta fara kafa gushen ginin
  • ‘Yan kasuwar sun koka akan yadda sababbin shagunan za su kawo cikas ga kasuwancinsu saboda a wurin suke ajiye ababen hawan da ake lodin kaya a cikin kasuwar

Kano - Babbar kotun jihar ta dakatar da gwamnatin jihar daga ci gaba da gina shaguna a hanyar da ke kasuwar Kofar Wambai a karkashin karamar hukumar Municipal, Daily Nigerian ta ruwaito.

An samu rahotanni akan yadda ‘yan kasuwar su ka dinga zanga-zanga akan ginin shagunan bayan gwamnatin ta sa tushen ginin.

Kano: Kotu ta hana Ganduje gina shaguna a hanyar Kasuwar Wambai
Kotu ta hana Gwamnan Kano Ganduje ya gina shaguna a hanyar kasuwar Wambai. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta rahoto cewa ‘yan kasuwar sun ce shagunan za su iya kawo cikas ga kasuwancinsu, saboda a inda aka fara kafa tushen ginin ne suke lodin kayan da ake wucewa dasu wurare daban-daban na kasar nan.

Bayan jin karar kotu ta dakatar da duka bangarorin daga amfani da filin

Bayan jin karar da ‘yan kasuwar su ka yi, a ranar Juma’a, Justice Aisha Ya’u ta bayar da umarni ga gwamnatin jihar, inda tace a dakata da ginin, har sai an gama shari’ar a shekara mai zuwa.

Ta umarci duka bangarorin da tsagaitawa daga amfani da filin har sai an kammala shari’ar.

Kotun ta ce:

“An dakatar da duk bangarorin guda biyu daga amfani da filin har sai an kammala shari’ar wurin.

“An dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Janairun 2022.”

Kotun ta amshi shari’ar ne bayan gabatar da kara a ranar 17 ga watan Disamban 2021 tare da rantsuwar kotu.

Lauyan ‘yan kasuwar ya yi korafi akan toshe hanyar da ginin ya yi

Lauyan ‘yan kasuwar, Sadiq Abdullahi ya yi korafi akan yadda gwamnatin jihar ta fara kafa tushen ginin wanda wurin hanyar wucewar jama’a ne.

Wani dan kasuwa, Anas Bala ya sanar da Daily Nigerian cewa bai dace gwamnatin ta yi gini a wurin ba saboda ta wurin ake sauke kaya kuma ta nan ‘yan kwana-kwana su ke wucewa idan bukatar hakan ta taso.

‘Yan kasuwa sun fito zanga-zanga domin hana Gwamnatin Ganduje kara shaguna a Wambai

A baya, ‘yan kasuwan Kofar Wambai sun buge da zanga-zanga a garin Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, a dalilin shirin kafa wasu shagun.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jama’a sun tashi da safe ne kurum suka ga ana aikin gina shagunan da za a raba ta kan hanyoyin da ake wucewa.

Masu zanga-zangar sun taru a layin Sani Buhari domin nuna rashin amincewarsu. A gefe guda kuma jami’an ‘yan sanda sun yi ta kokarin su tarwatsa su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel