‘Yan kasuwa sun fito zanga-zanga domin hana Gwamnatin Ganduje kara shaguna a Wambai

‘Yan kasuwa sun fito zanga-zanga domin hana Gwamnatin Ganduje kara shaguna a Wambai

  • ‘Yan kasuwan Kofar Wambai sun yi zanga-zanga domin nuna rashin goyon bayan gina wasu shaguna
  • Masu sana’a a wannan kasuwa sun ce idan aka raba shaguna tsakanin kanti, kasuwar za ta matse sosai
  • Gwamnati ta hakikance a kan bakarta, ta fara aiki kuma ta baza ‘yan sanda domin gudun tarzoma

Kano - ‘Yan kasuwan Kofar Wambai sun buge da zanga-zanga a garin Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, a dalilin shirin kafa wasu shagun.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jama’a sun tashi da safe ne kurum suka ga ana aikin gina shagunan da za a raba ta kan hanyoyin da ake wucewa.

Masu zanga-zangar sun taru a layin Sani Buhari domin nuna rashin amincewarsu. A gefe guda kuma jami’an ‘yan sanda sun yi ta kokarin su tarwatsa su.

Kara karanta wannan

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

Wani daga cikin ‘yan kasuwan, Ibrahim Yakasai ya shaidawa manema labarai cewa sun fito aiki ne kurum sai suka ga an kafa tubalin gina wasu shaguna.

Ibrahim Yakasai yace an fara wannan aiki ne cikin tsakar dare. A cewar ‘dan kasuwan, shagunan da za a gina, za su tare hanyoyin da mutane suka saba bi.

‘Yan kasuwa
Kasuwar kofar Wambai Hoto: @kabiru.garba.144
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba za mu tsora ta ba inji masu zanga-zanga

“Mun taru a nan ne domin mu nuna rashin amincewarmu, amma abin bacin ran shi ne gwamnati ta baza jami’an tsaro su na Harbin iska domin a ba mu tsoro.”
“Wannan ba zai ba mu tsoro ba. Babu mai hankalin da zai yi shaguna a nan. Mun tabbata gwamna bai san da wannan ba, wasu ne kurum da neman kudi.”
- Ibrahim Yakasai

Wannan Bawan Allah da sauran ‘yan kasuwa ire-irensa, sun bayyana cewa ba za su yarda da wannan salo da aka dauko ba, domin za a kara samun cunkoso.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki a gidaje a Kano

Ko a yanzu haka mutane da ‘yan kasuwa su na kukan cewa kasuwar ta Kofar Wambai ta cika sosai.

Wani ‘dan kasuwa, Kabiru Garba ya koka a Facebook, yace babu amfanin wannan aiki da gwamnati ta dauko, domin an tare hanyar da mutane suke wucewa.

"Babban layin kasuwar Kofar Wambai kenan, yanzu dan Allah meye amfanin wannan? Ace hanya ana gine ta, inda mutane suke wucewa."

– Kabiru Garba.

Jaridar ta nemi jin ta bakin ‘yan sanda da kuma gwamnatin jihar Kano, ta ko ina abin ya faskara.

Mu na bin gwamnati bashi - 'Yan kasuwa

A makon da ya shude aka ji cewa ‘Yan kasuwan da suke harkar man fetur, sun ce su na bin gwamnati bashin N50bn, wanda hakan ya sa jarinsu ya fara yin kasa.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwan na reshen jihar Kano, Musa Yahaya-Maikifi yace za a dawo ganin layin fetur a gidajen mai idan gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel