Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno

Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno

  • A yau Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki garin Maidguri da ke jihar Borno
  • Gwamna Zulum ya yi kira ga 'yan jihar da su fito kwai da kwarkwata wurin tarar shugaban kasan a jihar saboda ya cancanci hakan
  • Zulum ya ce Buhari zai kaddamar da ayyukan tituna a jihar kuma ya cancanci jinjina ganin kokarin da yayi wurin dawo da zaman lafiya da tsaro

Maiduguri, Borno - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis zai ziyarci babban birnin jihar Borno, Maiduguri, cewar Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Zulum wanda ya sanar da hakan yayin da ya je duba aikin gadar sama ta Maiduguri, ya yi kira ga mazauna jihar da su fito kwansu da kwarkwata wurin karbar Shugaban kasa Buhari hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya roki mutanen jihar Borno su fito su tarbi shugaba Buhari da soyayya

Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno
Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce shugaban kasan zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da suka hada da gadar sama da kuma tituna. Zai kaddamar da CDL na jami'ar Maiduguri.

Zulum ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tushen ayyuka da shirye-shirye wadanda suka bayar da gudumuwa ta gari ga rayuwar 'yan jihar.

Gwamnan ya ce Buhari ya bayar da fifiko wurin dawowar zaman lafiya da tsaro tare da inganta rayuwar 'yan jihar.

Ya ce Buhari ya samar da dukkan goyon bayan da ya dace domin tabbatar da dawowar wutar lantarki a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

"Shugaban kasan ya cancanci jinjina ganin yadda ya amince da fitar da miliyoyin daloli domin siyan makamai da sauran kayayyakin bukatar sojoji da sauran hukumomin tsaro don yaki da ta'addanci," ya ce.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci

A wani labari na daban, kungiyar hadin kan Arewa, ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa akan nuna tausayi ga wadanda ta’addanci ya shafi yankinsu.

TheCable ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Litinin wacce Emmanuel Yawe, Sakataren watsa labaran kungiyar ACF ya saki, ya yi alawadai da kisan mutane 38 na karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Kungiyar ta bukaci Buhari, gwamnoni da sauran shugabannin arewa da su yi iyakar kokarinsu wurin nuna kula ga wadanda lamarin ya ritsa da su, Daily Trust ta ruwaito haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel