Gwamna Zulum ya roki mutanen jihar Borno su fito su tarbi shugaba Buhari da soyayya

Gwamna Zulum ya roki mutanen jihar Borno su fito su tarbi shugaba Buhari da soyayya

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya roki al'umma su fito da yawansu su yi wa shugaban ƙasa Buhari kyakkyawan maraba
  • Zulum yace shugaba Buhari zai kawo ziyara Borno ranar 23 ga watan Disamba domin kaddamar da wasu ayyuka
  • Daga cikin muhimman ayyukan da ake tsammanin Buhari zai bude, akwai gada ta farko a jihar Borno

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya yi kira ga al'ummar jihar Borno su fito kwansu da kwarkwata su tarbi mai girma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar 23 ga watan Disamba, 2021.

This Day ta rahoto cewa ana tsammanin shugaban ƙasan, yayin ziyararsa zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Zulum ta kammala.

Gwamna Zulum ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido a ɗaya daga cikin ayyukan da ake shirin bude wa, wata gadar sama da yammacin jiya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi karin bayani kan zuwansa Legas maimakon zuwa ta'aziyya Sokoto

Zulum.da Buhari
Gwamna Zulum ya roki mutanen jihar Borno su fito su tarbi shugaba Buhari da soyayya Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Zulum yace shugaban ƙasa Buhari ya tallafawa jihar Borno wajen samar da zaman lafiya tsakanin mutane da kuma kawo cigaba.

Muna kokarin gyara lantarki a Borno - Zulum

Ya ƙara da cewa Buhari ya kashe sama da dala miliyan $50m wajen ganin mutanen jihar Borno sun samu hasken wutar lantarki.

Farfesan ya kuma yi alƙawarin cewa da zaran gwamnati ta kammala aikin tashar Lantarki ta Maiduguri Gas Power Plant a watan Maris, al'umma za su samu wuta ba kakkautawa na tsawon awa 24 kullum.

"Da zaran mun kammala aiki a tashar wutar lantarki ta Maiduguri, Mutanen Borno za su ga haske awa 24 ba ɗauke wa," inji shi.

Zulum ya yaba wa Buhari

Kazalika Zulum ya yaba wa shugaban ƙasa bisa lale makudan kudi wajen samar wa sojojin makamai da kayan aiki don kara musu ƙarfin guiwa a yaki da yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

Ya yaba wa shugaban bisa umartan sojojin su tsaftace yan ta'adda daga yankunan gonakin mutane, domin baiwa manoma damar cigaba da sana'arsu.

Vanguard tace Yayin ziyarar Buhari a Borno, ana tsammanin zai kaddamar da gada ta farko a jihar Borno da sauran wasu muhimman ayyuka.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya yi karin bayani kan zuwansa Legas maimakon zuwa ta'aziyya Sokoto

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kare kansa daga sukar da yake sha bayan zuwa Legas a lokacin da aka kashe mutane a Sokoto.

Malam Garba Shehu, yace ba kaddamar da littafi ya kai Buhari Legas ba, ainihin makasudin zuwansa dan jiragen ruwan sojoji ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel