Bayan shekara 6 da hawan Buhari mulki, Malamin makaranta yace har gara Jonathan

Bayan shekara 6 da hawan Buhari mulki, Malamin makaranta yace har gara Jonathan

  • Dr. Muhsin Ibrahim, malamin makaranta ne a Arewacin Najeriya, ya na cikin matasa masu magana da tsoma baki a kan halin da al’umma su ke ciki
  • Kwararren malamin wasan kwaikwayon ya yi wata ‘yan magana kwanaki a shafinsa na Facebook, wanda ta bar mutane da tofa albarkacin bakinsu
  • Ganin kashe-kashen da aka yi a Sokoto, malamin jami’ar yace gara shugaba Jonathan a kan Muhammadu Buhari, yace Buhari bai nuna tausayin talaka

Muhsin Ibrahim ya yi karatun ilmin harshe a jami’ar Bayero da ke Kano da kuma jami’ar Universität zu Köln a kasar Jamus, inda ya yi PhD a 2021.

Da yake Allah-wadai da gwamnatin Najeriya, Dr. Muhsin yace ya na ganin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fi Muhammadu Buhari sanin mulki.

“Ko da ba na yabon shiririta, amma na gamsu cewa (tsohon shugaban kasa) Goodluck Jonathan ya fi shugaban kasa (Muhammadu Buhari).

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

“Ko ba komai, ya fi shi nuna damuwa da tausayi. Shi kuwa Buhari bai damu da duk abin da za a fada a game da shi ko kuwa gwamnatinsa ba.”
“Mutumin nan ya na cika burinsa ne kurum, ya na kuma more tsufar rayuwarsa.” – Muhsin Ibrahim.
Malamin makaranta
Dr. Mushin Ibrahim ya na kira a kare Arewa Hoto: @muhsin2008
Asali: Facebook

Martanin da mutane su ke badawa a Facebook

Ba a bar malamin haka nan ba, wasu sun maida masa martani, yayin da wasu suka yarda da shi, wasu kuma suka ce jirgi daya ya dauko Buhari da Jonathan.

“Ka cika saurin mantuwa. Jonathan da ya je Kano ya na rawar kamfe, yayin da Boko Haram ke tarwatsa Arewa maso gabas da bama-bamai. Abin da nake gani yau da mamaki, duk ba su da tausayin talaka, kuma ba su san halin da kasa ta ke ciki ba.”

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

- Muhammad A. Abdallah

“Da a Disamban 2014 ka fadi wannan magana, da an kira ka arne ko kafiri. Yanzu dai duk mun yarda ba a taba yin shugaban da ya gaza a tarihi irin Buhari ba.”

- Abdulrahman Gusau

Buhari kan shi kurum ya sani, don haka bai da tausayi. Jonathan bai san inda ya dosa ba, amma ya kan fahimci kokenmu. Ya damu da halin da mu ke ciki a lokacin.

- Fatima Abbas

“Gazawar Buhari ba za ta sa a wanke Jonathan ba. GEJ ya yi sakaci wajen yakar Boko Haram, ya siyasantar da lamarin ko a lokacin da ake kashe mutane. Ya tika rawa a lokacin da aka dasa bam, ina tausayi a nan?

- Habib Abdallah

Da hannun jami'am tsaro

A makon nan ne aka ji mataimakin shugaban majalisar wakilai, Ahmad Wase ya na zargin ‘Yan Sanda da laifi a matsalar rashin tsaro, yace su na taimakawa miyagu.

Kara karanta wannan

Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

Hon. Wase ya kawo hujjojin da ke fallasa rashin gaskiyar bara-gurbin ‘Yan Sanda. 'Dan majalisar yace ana samun 'yan sanda su na fito da marasa gaskiya da aka kama

Asali: Legit.ng

Online view pixel