Ganduje ya aike wa Kwankwaso sakon ta'aziyyar rasuwar dan uwansa

Ganduje ya aike wa Kwankwaso sakon ta'aziyyar rasuwar dan uwansa

  • Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da sakon ta'aziyyarsa ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon ubangidansa
  • Ganduje ya kwatanta rasuwar dan uwan Rabiu Musa Kwankwaso da babban rashi ga iyalinsa, jihar Kano da kasar Najeriya baki daya
  • A jiya Laraba ne labarin rasuwar dan uwan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Injiniya Inuwa Kwankwaso ya karade gari

Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi wa tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa-Kwankwaso, Inuwa Musa-Kwankwaso.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sakon ta'aziyyar na kunshe a wata takarda da kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Talata a Kano.

Ganduje ya aike wa Kwankwaso sakon ta'aziyyar rasuwar dan uwansa
Ganduje ya aike wa Kwankwaso sakon ta'aziyyar rasuwar dan uwansa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ganduje ya kwatanta mutuwar Injiniyan aikin noman da babban rashi ga 'yan uwansa, jiha da kasar baki daya, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Shekara 1 da rasuwar Mahaifinsa, Kwankwaso ya rasa babban ‘danuwansa a Duniya

"Ya kebance kansa a matsayin ma'aikacin gwamnati mai sadaukarwa kafin ya yi murabus, ballantana lokacin da ya yi aiki a shirin gandun daji inda ya kwashe shekaru masu yawa," Garba ya ce a cewar Ganduje.

Ganduje ya yi fatan Allah ya sanya Inuwa a Aljanna kuma ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashin.

Gwamna Ganduje tsohon mataimakin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne lokacin da ya ke gwamnan jihar Kano.

Shekara 1 da rasuwar Mahaifinsa, Kwankwaso ya rasa babban ‘danuwansa a Duniya

A wani labari na daban, daya daga cikin ‘yanuwan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, watau Kwamred Inuwa Musa ya rasu dazun nan.

Sanarwar rasuwar wannan Bawan Allah ta fito daga kakakin cibiyar yada labarai ta Kwankwasiyyya, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Kano ba zai raba mun hankali ba, Gwamna Ganduje

Hadimin tsohon Ministan tsaron, Saifullahi Hassan ya tabbatar da labarin, ya na mai yi masa addu’a, da karawa da cewa lallai mutumin kirki ne.

“Cikin fawwala lamari ga Allah madaukakin Sarki (SWT), mu na bada sanarwar rasuwar Kwamred Inuwa Musa Kwankwaso.
“Shi ne kani mai bi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya (Dr.) Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.” - Bature Dawakin Tofa.

Daily Trust tace Inuwa Musa Kwankwaso ya rasu ne bayan ya yi ta fama da rashin lafiya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Marigayin ya yi aikin gwamnati a matsayin injiniyan gona a garuruwa dabam-dabam, daga ciki har da birnin Ibadan da wasu wurare a kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel