Shekara 1 da rasuwar Mahaifinsa, Kwankwaso ya rasa babban ‘danuwansa a Duniya

Shekara 1 da rasuwar Mahaifinsa, Kwankwaso ya rasa babban ‘danuwansa a Duniya

  • A ranar Litinin dinnan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya rasa daya daga cikin manyan ‘yanuwansa
  • Kwamred Inuwa Musa Kwankwaso ya rasu bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya a asibitin AKTH

Marigayin da ya rasu ya na mai shekara 64 shi ne wanda yake bin tsohon Gwamnan jihar Kano a gidansu

Kano - Daya daga cikin ‘yanuwan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, watau Kwamred Inuwa Musa ya rasu dazun nan.

Sanarwar rasuwar wannan Bawan Allah ta fito daga kakakin cibiyar yada labarai ta Kwankwasiyyya, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Hadimin tsohon Ministan tsaron, Saifullahi Hassan ya tabbatar da labarin, ya na mai yi masa addu’a, da karawa da cewa lallai mutumin kirki ne.

“Cikin fawwala lamari ga Allah madaukakin Sarki (SWT), mu na bada sanarwar rasuwar Kwamred Inuwa Musa Kwankwaso.”

Kara karanta wannan

Babban Basarake ya mutu a Kaduna, Buhari da Gwamna El-Rufai sun aiko sakon ta’aziyya

“Shi ne kani mai bi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya (Dr.) Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.” - Bature Dawakin Tofa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso ya rasa babban ‘danuwansa a Duniya
Kwankwaso da Marigayi Inuwa Musa
Asali: UGC

Daily Trust tace Inuwa Musa Kwankwaso ya rasu ne bayan ya yi ta fama da rashin lafiya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Wanene Marigayi Inuwa Musa?

Marigayin ya yi aikin gwamnati a matsayin injiniyan gona a garuruwa dabam-dabam, daga ciki har da birnin Ibadan da wasu wurare a kasar Amurka.

Injiniya Inuwa Musa Kwankwaso ya yi ritaya daga aiki tuni, ya bar Duniya a ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, 2021, ya na mai shekara 64 da haihuwa.

Rahoton yace wannan Bawan Allah ya bar mata daya da ‘ya ‘ya biyu mata – Barista Nafisa Inuwa da Zainab Inuwa, da kuma tarin ‘yanuwa na kusa da nesa.

Kara karanta wannan

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

Tuni dai an birne Inuwa a kauyensu na Kwankwaso da ke cikin karamar hukumar Madobi, jihar Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya yi tanadi.

Inuwa ya bi Majidadi gidan barzahu

A daidai irin wannan lokaci a shekarar bara, aka ji cewa Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman lasar karaye, Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa.

Marigayi Musa Saleh mai shekara 93, shi ne mahaifinsu tsohon gwamnan Kano kuma daya daga cikin wadanda suka dade su na sarauta a masarautar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel