Sarki a arewacin Najeriya ya koka kan kwace masarautarsa da 'yan bindiga suka yi

Sarki a arewacin Najeriya ya koka kan kwace masarautarsa da 'yan bindiga suka yi

  • Muhammad Haruna, Sarkin Wase ya koka kan yadda 'yan bindiga suka kwace rabin masarautarsa ta Wase da ke jihar Filato
  • Kamar yadda basaraken ya sanar, wannan rashin tsaron zai iya kawo rashin abinci ga kasar nan ganin cewa ba su iya noma saboda ta'addancin
  • Sarkin ya ce an cinye kashi saba'in na kayan abinci da aka girbe a yankin, hakan yasa abinci yayi tsada tun a damina, ta yuwu ya sake tashi da rani

Wase, Filato - Sarkin Wase, Muhammad Haruna ya ce akwai yuwuwar jihar Filato da ke Najeriya ta fuskancin karancin abinci sakamakon yadda rashin tsaro ya hana manoma masu tarin yawa zuwa gonakinsu.

Sarkin ya koka da yadda 'yan ta'adda suka kwace kusan rabin karamar hukumar Wase da ke jihar kuma jama'a ba su iya zuwa gona ko kuma ayyukan gona, kusan kashi saba'in na kayan abincin da aka noma an siyar da shi kafin damina mai zuwa, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga

Sarki a arewacin Najeriya ya koka kan kwace masarautarsa da 'yan bindiga suka yi
Sarki a arewacin Najeriya ya koka kan kwace masarautarsa da 'yan bindiga suka yi. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

The Nation ta ruwaito cewa, basaraken mai daraja ta farko, ya bayyana hakan a jiya a garin Jos yayin taron da kungiyar 'yan jarida ta shirya. Ya koka da yadda mazauna Wase yanzu suke rayuwa cikin tsoron 'yan ta'addan wadanda suka kwace rabin garin Wase.

A kalamansa: "Ni manomi ne kuma da yawan jama'ar da nake mulka manoma ne. A saboda rashin tsaro, da yawanmu mun bar kauyukanmu zuwa birni domin neman abun rufawa kai asiri saboda ba za mu iya zuwa gona ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna cikin watan Disamba ne. Masara yanzu a Wase buhun ta ya kai dubu ashirin da takwas. Ka kwatanta nawa za ta kai a watan Afirilu. Mai kudi ne ke iya siyan shinkafa buhu dubu ashirin da shida ko asirin da bakwai.
"Matsalar da za mu iya samu a Filato nan gaba ko kuma Najeriya baki daya, shi ne yunwa, wanne hali za a shiga lokacin da ba na damina ba?"

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

An sake samun gawar wani basarake da aka sace a Imo

A wani labari na daban, jama'ar yankin Ihitte Ihube da ke karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo sun shiga cikin jimami da dimuwa bayan samun gawar basarake Eze Pau Ogbu da aka yi.

A ranar Lahadi, an sace Eze Ogbu da wani shugaban matasa an sace su bayan an kone fadarsa da wasu ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Amma an samo gawarsa a ranar Laraba kuma an aika da ita fadarsa yayin da ake shirin birne shi, SaharReporters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel