Da duminsa: IGP ya mika rahoton binciken Abba Kyari da Hushpuppi gaban PSC

Da duminsa: IGP ya mika rahoton binciken Abba Kyari da Hushpuppi gaban PSC

  • Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda za ta tattauna dangane da batun Abba Kyari, Shugaban IRT da aka dakatar
  • Wannan ya biyo bayan mika rahoton binciken Kyari da sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya gabatar gaban hukumar
  • A ranar Lahadi 19 ga watan Disamba, aka samu wannan rahoton daga dan jarida kuma jami’in PSC, Braimoh Adogame Austin

Abuja - Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Usman, ya gabatar da takardun rahotanni gaban hukumar ‘yan sanda dangane da shugaban rundunar IRT, Abba Kyari wanda aka dakatar.

The Nation ta bayyana yadda wani jami’in PSC, Braimoh Adogame Austin. a ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba ya ce hukumar za ta zauna ta tattauna akan rahoton.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

Da duminsa: IGP ya mika rahoton binciken Abba Kyari da Hushpuppi gaban PSC
Da duminsa: IGP ya mika rahoton binciken Abba Kyari da Hushpuppi gaban PSC. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa, an samu inda Austin ya kada baki yace:

“IGP ya gabatar da rahotanni akan Abba Kyari ga PSC kuma za a fara tattaunawa dangane da lamarin a wannan makon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba zan iya fadar yaushe aka gabatar da rahoton ba amma yanzu haka ya na hannun hukuma.”

Abba kyari ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa

Sai dai an samu bayanai akan yadda Kyari ya amsa tambayoyi akan zarginsa da damfarar dala miliyan 1.1 da wani fitaccen dan Instagram, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

FBI ta zargi yadda Hushpuppi ya hada kai da Kyari wurin kama wani abokin harkarsa, Chibuzo Vincent, don barazanar fallasa damfarar dala miliyan 1.1 da ya yi ga wani dan kasuwar Qatar.

FBI ta Amurka ta ce Hushpuppi ya tura dala 20,600 cikin asusun bankin Kyari.

Kara karanta wannan

Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna

Sakamakon haka ne PSC ta dakatar da Kyari sannan ta samar da kwamiti na musamman don bincike (SIP) akan gano ko Kyari ya na da hannu a damfarar.

Yanzu haka batun Kyari ya na gaban kwamitin horarwa (FDC), an samu wannan daga wani babban jami’i wanda bai bayyana sunansa ba.

Yayin bayar da bayani akan lamarin, babban jami’in ya bayyana yadda Kyari ya bayar da bayanai, inda ya ce yanzu ne kwamitin za ta san matakin da za ta dauka dangane da amsoshinsa da kuma bayanan da ke SIP.

Makomar babban jami’in na kasa tana dabo, ana jiran abinda kwamitin zai zartar.

Hushpuppi: IGP ya mika tuhuma ga Abba Kyari, Malami na duba bukatar mika shi Amurka

A wani labari na daban, Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya tuhumi kwamandan rundunar IRT, Abba Kyari, kan alakar da aka gano ya na da ita da Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, gagarumin dan damfarar yanar gizo.

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

Daily Trust ta ruwaito cewa, ofishin antoni janar na tarayya na bukatar a duba bukatar da Amurka ta turo na bada fitaccen dan sandan domin bincike.

Daily Trust a ranar Lahadi ta gano cewa an mika tuhumar ne bayan binciken da wata kwamitin bincike ta yi, wacce ta bankado al'amuran da ke faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel