Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna

Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna

  • Mutane tara sun rasa rayukansu a Chikun, Zangon Kataf, Igabi da karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna
  • Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a
  • A cewarsa, rundunar hadin guiwa ta sojoji da ‘yan sanda ne su ka sanar da kashe-kashen ga gwamnatin jihar

Kaduna - Rahotanni sun bayyana yadda mutane 9 su ka rasa rayukansu a karamar hukumar Igabi, Chikun, Zangon Kataf da Zaria a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna
Rayuka 9 sun salwanta sakamakon farmakin da miyagu suka kai Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa ‘yan bindiga sun halaka mutane uku a sashin Buruku-Udawa, hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari a karamar hukumar Chikun.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa

A cewarsa, wani mutum ya samu rauni sakamakon harbin bindiga kuma ya na asibiti, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aruwan ya ce a hanyar Yola-Kadi da ke karamar hukumar Chikun, ‘yan bindigan sun halaka mutum daya sannan sun ji wa dayan rauni.

Ya kara da bayyana yadda ‘yan bindigan su ka halaka mutane biyu a kauyen Sako, da ke karamar hukumar Zangon Kataf, an kuma tsinci gawawwaki biyu a wani sintiri da ‘yan bindiga su ka yi a wuraren Kurfi zuwa Magamiya.

A karamar hukumar Zaria kuma sun halaka wani Alhaji Habibu a kauyen Saye.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa kan rahoton inda ya yi wa wadanda su ka rasa rayukansu fatan samun rahama, sannan ya yi wa wadanda su ka ji rauni fatan samun lafiya.

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

A wani labari na daban, wata waka ta kwarzantawa tare da yaba wa fitaccen dan bindiga, Bello Turji, tana yawo a halin yanzu a arewacin Najeriya cikin mutanen da suke fama da cin zarafi tare da rashin kwanciyar hankalin da 'yan bindigan suke saka yankin.

Turji, wanda dan asalin garin Shinkafi ne daga jihar Zamfara, shi ne shugaban 'yan ta'addan da ke addabar jihohin Sokoto, Zamfara da wani sashi na jamhuriyar Nijar.

'Yan ta'addan ke da alhakin kisa da hana daruruwan jama'a sakat a yankin, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel