Hushpuppi: IGP ya mika tuhuma ga Abba Kyari, Malami na duba bukatar mika shi Amurka

Hushpuppi: IGP ya mika tuhuma ga Abba Kyari, Malami na duba bukatar mika shi Amurka

  • Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Alkali Usman Baba, ya mika takardar tuhumar ga fitaccen dan sanda Abba Kyari
  • Rahoton kwamitin bincike ya nuna cewa tabbas akwai sadarwa tsakanin Abba Kyari da rikakken dan damfara Hushpuppi
  • Hakazalika, antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya na duba bukatar yuwuwar mika dan sandan Amurka

Abuja - Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya tuhumi kwamandan rundunar IRT, Abba Kyari, kan alakar da aka gano ya na da ita da Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, gagarumin dan damfarar yanar gizo.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ofishin antoni janar na tarayya na bukatar a duba bukatar da Amurka ta turo na bada fitaccen dan sandan domin bincike.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun mamaye murabba'in mita 1,129 na gandun dajin Najeriya

Hushpuppi: IGP ya na tuhumar Abba Kyari, Malami na duba bukatar mika shi Amurka
Hushpuppi: IGP ya na tuhumar Abba Kyari, Malami na duba bukatar mika shi Amurka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust a ranar Lahadi ta gano cewa an mika tuhumar ne bayan binciken da wata kwamitin bincike ta yi, wacce ta bankado al'amuran da ke faruwa.

Wata kotun Amurka ta na tuhumar Kyari da hada kai tare da karbar $1.1 miliyan kan wata damfara da Hushpuppi yayi wa wani dan kasuwar Qatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar kula da lamurran 'yan sanda ta dakatar da Kyari daga matsayinsa na mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar ta musamman ta IRT sakamakon bukatar da Alkali ya mika.

An gano cewa, kwamitin bincike da ya samu shugabancin DIG Joseph Egbunike, wanda ya mika rahoton bincikensa a watan Augusta, ya tabbatar da cewa an samu sadarwa tsakanin Kyari da dan damfarar.

"Sifeta Janar na 'yan sanda ya mika takardar tuhuma ga Abba Kyari sakamakon binciken da aka yi a kan shi. Kwamitin ya gano cewa an samu sadarwa tsakanin Kyari da Hushpuppi wanda ya yi karantsaye ga aikin dan sanda," wata majiya babba ta tsaro ta sanar da Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tuhumar FBI: Buhari ne zai yanke hukunci kan Abba Kyari, Ministan harkokin yan sanda

Ya ce, sai dai, kwamitin bai bada shawarar a mika Kyari ga Amurka ba saboda ba a ga wani laifi da fitaccen dan sandan yayi wa Amurka ba.

"Babu wata shaida da ke nuna cewa akwai laifin da dan sanda yayi wa Amurka da ya dace a mika shi kasar. Hukumomin da suka dace ne za su ladabtar da shi.
"Sai dai kuma, AGF zai bada shawarar ko za a mika shi Amurka, wanda da wuya hakan ta faru," ya kara da cewa.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Frank Mba a wata tattaunawa da yayi a waya, ya ce kamar yadda aikin 'yan sanda ya ke, sifeta janar ya mika shawarar kwamitin binciken ga hukumar kula da ayyukan 'yan sanda domin daukan matakin da ya dace.

2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa

A wani labari na daban, jam’iyyar APC ta ce ba ta tabbatar wa da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan tabbacin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, kamar yadda ake ta yadawa.

Kara karanta wannan

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sakataren CECPC, John Akpanudoedehe ya bayyana hakan a wata takarda a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce komawar mutum jam’iyya ba ya bayar da tabbacin a bashi wani matsayin a jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel