Luguden wutan sojoji: Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasakar neman sulhu ga shugaba Buhari

Luguden wutan sojoji: Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasakar neman sulhu ga shugaba Buhari

  • Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi yankunan jihar Zamfara, Bello Turji. ya nemi a sulhu da gwamati da sarakunan gargajiya
  • Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin sama da ƙasa sun ƙara ƙaimi kan yan bindiga bayan kotu ta ayyana su yan ta'adda
  • Turji ya rubuta wasikar sulhu da zaman lafiya mai adireshin shugaba Buhari, gwamna Matawalle da kuma sarkin Shinkafi

Zamfara - Ƙasurgumin ɗan bindiga wanda ya addabi jihar Zamfara da Sokoto, Bello Turji, ya bukaci yin sulhu da masu rike da mukaman siyasa da sarakunan gargajiya a jiharsa ta Zamfara.

Dailytrust tace Turji ya yi alkawarin aje makamansa domin dakatar da zubar da jini amma bisa sharaɗin sulhu tsakanin bangarensa da bangaren gwamnati.

A watan da ya gabata ne, bayan babbar kotun tarayya ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda, gwamnatin tarayya ta lashi takobin kawo ƙarshen yan ta'adda baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Babu ɗan ta'addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan ya sha alwashi

Bello Turji
Luguden wutan sojoji: Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasakar neman sulhu ga shugaba Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wasikar mai ɗauke da adireshin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, gwamna Bello Matawalle, da sarkin Shinkafi, kuma ɗauke da kwanan watan 14 ga Disamba ta isa garin Shinkafi ta hannun ɗan aiken Turji.

Wani mazaunin garin Shinkafi, wanda ke ɗaya daga cikin yan kwamitin zaman lafiya, ya tabbatar da ingancin wasikar mai shafi uku ga jaridar Dailytrust.

Wannan ba shine na farko ba Turji ke tura sakon wasika zuwa ƙauyuka ba, domin ko a watan Satumba ya rubuta takardan haɗin guiwa da wani jagoran yan bindiga, Halilu Sabubu, inda suka gargaɗi mutane kan kawo hare-hare.

Luguden wutan sojoji ta sama da ƙasa

Wannan na zuwa ne yayin da dakarun hukumomin tsaron Najeriya suka ƙara matsa ƙaimi wajen kai hare-hare maɓoyar yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas

Matsin lambar dakarun sojin sama da ƙasa ya yi sanadiyyar tarwatsa yan bindigan a maɓoyarsu, tare da hallaka wasu da dama.

Sai dai masu sharhi kan matsalar tsaro na ganin wannan yunkurin na Turji ba zai yi ƙarko ba duba da yadda shirin sulhu na gwamnatin Zamfara da Katsina ya lalace tun ba'a je ko ina ba a baya.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a makon da ya gabata, ruwan wutan sojojin sama kan yam bindiga dake bayan Halilu, "Ya kashe su da yawa, wasu dama suka jikkata."

Haka nan kuma sojoji sun sake kai hari ta sama da ƙasa kan yan ta'addan a wasu yankunan ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni, jihar Sokoto da kuma Shinkafi a Zamfara.

Yayin wannan harin, dakarun sojin sun samu nasarar aika da yawan su zuwa Lahira, yayin da wasu kuma suka tsere domin ceton rayuwarsu.

Meyasa ya ɗauki makami tun farko?

Kara karanta wannan

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Turji, da wakar yabo

A wasikar da ya rubuta, Turji, ya bayyana ainihin dalilin ɗaukar makaminsu da cewa ya samo asali ne daga rashin adalci da kuma kashe mutanen su da ake yi.

Yace duk wasu kashe-kashe da yan bindiga ke yi na waɗanda ba su ji ba ba su gani ba zasu kawo karshe da yardar Allah.

Sai dai tun kafin wasikar Turji, Rahotanni sun bayyana cewa gawutaccen ɗan ta'addan na shirin mika wuya biyo bayan matsin lambar da yake sha daga wurin abokansa jagororin yan bindiga.

Shin wannan ne karon farko?

Tun a watan Nuwamba, wasu daga cikin yan bindiga suka fara aje makaman su domin yin sulhu da mutanen ƙauyuka a Zamfara.

A watan da ya shude, Dailytrust ta ruwaito yadda ɗan bindiga mai hatsari, Ali Kachalla ya yi sulhu da Masarautar Ɗansadau a jihar Zamfara.

Wazirin Ɗansadau, Alhaji Mustapha Umar, ya tabbatar da haka, yace Ali Kachalla ya amince ya rungumi zaman lafiya da aje makami.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja

Wasu tsagerun yan bindiga sun sace jami'in hukumar yan sanda ta farin kaya (DSS) a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kashe wani jami'in sa'kai ɗan bijilanti guda ɗaya yayin harin na ranar Asabar da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel