Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanin Dangote, BUA da wasu tallafin kudi N30bn

Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanin Dangote, BUA da wasu tallafin kudi N30bn

  • Babban bankin Najeriya, a yunkurinsa na bunkasa samar da sukari zai saki Naira biliyan 30 ga kamfanoni daban-daban
  • Shugaba Buhari ne ya amince da shirin kuma an nufi kara yawan samar da sukarin da Najeriya ke samu ne a yanzu
  • Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu sune manya biyu da suke cikin wadanda za su ci gajiyar harkar sukari a Najeriya

Abuja - Dala miliyan 73 da Gwamnatin Tarayya ta ware don ba da tallafi a harkar sukari, mai yiyuwa ne zai taimaka wa kamfanonun sukarin Dangote, da BUA, da sauran masu taka rawa a fannin samar da sukari.

Babban Bankin Najeriya (CBN) zai raba dala miliyan 73 (N30.7bn) a madadin gwamnati don taimakawa wajen gina masana'antar sukari a Najeriya.

Sukarin amfani na yau da kullum
Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanin Dangote, BUA da wasu tallafin kudi N30bn | Hoto: GettyImages

Shirin wanda ke da taken, tallafin shugaban kasa kan samar da ayyukan noman rani don dakile koma baya, zai samar da ayyukan noman rani a hekta 10,000 na noman sukari.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

Za a gina wuraren ne a yankuna shida a Arewacin Najeriya, kamar yadda gwamnati ta jaddada kudirinta na aiwatar da babban shirin bunkasa sukari na kasa, inji rahoton The Cable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me Ministan ke cewa?

Da yake karin haske kan yadda shirin na gwamnati yake, minstan cinikayya na Najeriya Niyi Adebayo ya ce:

"Shirin ya kunshi kafa asusun ba da tallafin ban ruwa na dala miliyan 73 ga masu cin gajiyar shirin tsallafin samar da sukari."

Ya ci gaba da cewa:

“Manufar ita ce a ba da tallafin samar da ayyukan noman rani a gonakin noman sukari hekta 10,000 a Numan, Jihar Adamawa, Sumti, Jihar Neja, Lafiagi, Jihar Kwara, Bacita, Jihar Kwara, da Toto da Tunga, duk a Jihar Nasarawa.”

Martanin Dangote game da wadatar sukari a Najeriya

A watan Oktoba, Aliko Dangote ya yi kira ga Najeriya da ta dawo kan tsarinta na sukari, wanda idan aka bi shi, zai ceto Najeriya daga kudade tsakanin dala miliyan 600 zuwa dala miliyan 700 a duk shekara a matsayin kudin hada-hadar waje.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

A wani labarin, tattalin arzikin Najeriya ya yi asarar N499.32bn sakamakon rufe shafin Twitter tun daga ranar 4 ga Yuni, 2021.

A ranar 4 ga watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da Twitter bayan da kafar ta goge sakon da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter, inji rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel