Da duminsa: Buhari ya aminta a biya likitoci albashinsu da aka rike lokacin yajin aiki

Da duminsa: Buhari ya aminta a biya likitoci albashinsu da aka rike lokacin yajin aiki

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da biyan ma’aikatan lafiya wadanda aka rike wa albashi tsawon watanni sanadin haka ya sa suka je yajin aiki
  • Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da su ka yi da shugaban kasa a Abuja
  • A cewar ministan, Buhari ne ya bayar da umarni ga ma’aikatar kudi, akan biyan likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya na lokacin da suke yajin aiki a tsakanin 2018 da 2021

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da biyan ma’aikatan lafiya albashinsu wanda aka rike lokacin da suke yajin aiki.

Chris Ngige, ministan kwadago da ayyuka ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai bayan sun yi wani taro da shugaban kasa a gidan gwamnati da ke Abuja, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 6 da hawan Buhari mulki, Malamin makaranta yace har gara Jonathan

Da duminsa: Buhari ya aminta a biya likitoci albashinsu da aka rike lokacin yajin aiki
Da duminsa: Buhari ya aminta a biya likitoci albashinsu da aka rike lokacin yajin aiki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewar ministan, Buhari ya bayar da umarni ga ma’aikatar kudi, kasafi da tsari inda ya bukaci a biya likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya albashinsu na watannin da su ka yi yajin aiki tsakanin 2018 da 2021, Channels Tv ta ruwaito.

“Shugaban kasa ya amince a makon da ya gabata kuma an bayar da umarni ga ma’aikatar kudi akan ta saki albashin likitoci masu kwarewa na watan Satumba da Oktoban 2021, wanda da aka rike musu,” a cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Har ila yau, amincewar ta hada da na mambobin JOHESU wadanda su ka je yajin aiki a 2018 na watanni uku. Bayan watan farko, bayan watan Maris lokacin ba su koma ba, sai muka bukaci a dakatar da biyansu albashi. Wannan sanannen abu ne, za ka iya yin yajin aiki amma wanda ya dauke ka aiki ya na da damar dakatar da biyan shi.

Kara karanta wannan

Ba dan Buhari ba da tuni Najeriya ta zama daular muslunci, inji Lai Mohammed

“Don akan wadannan kudin na Afirilu da Mayun 2018 , shugaban kasa ya kara amince wa ma’aikatar kudi akan ta biyasu kudadensu.
“Wannan ya biyo bayan yadda ma’aikatan lafiya da dama suka jajirce lokacin da annobar COVID-19 ta barke kuma duk da haka ba a kara musu wani alawus ba akan asalin na annoba.”

Dalilin da yasa muka janye yajin aiki bayan shafe watanni biyu muna fafatawa, Likitoci

A wani labari na daban, Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta bayyana dalilinta na janye yajin aikin da ta kwashe kwanaki 63 tana yi, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Yajin aikin NARD, wanda ya shafe sama da watanni biyu ya jefa asibitocin gwamnati da kuma marasa lafiya cikin mummunann yana yi.

Sabon shugaban NARD, Godiya Ishaya, wanda ya tabbatar da janye yajin aikin, yace sun ɗauki matakin ne bayan taron kwamitin zartarwa na ƙungiyar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

Asali: Legit.ng

Online view pixel