Dalilin da yasa muka janye yajin aiki bayan shafe watanni biyu muna fafatawa, Likitoci

Dalilin da yasa muka janye yajin aiki bayan shafe watanni biyu muna fafatawa, Likitoci

  • Bayan kwanaki sama da 60 tana yajin aiki, Kungiyar likitoci NARD, ta sanar da janye yajin aiki bayan taronta na ranar Lahadi
  • NARD bisa jagorancin sabbin shugabanninta da aka zaɓa, ta ɗauki wannan matakin ne domin baiwa gwamnati lokaci
  • A cewar likitocin, sun fahimci an samu cigaba daga ɓangaren gwamnati wajen kokarin cika musu bukatunsu

Abuja - Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta bayyana dalilinta na janye yajin aikin da ta kwashe kwanaki 63 tana yi, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Yajin aikin NARD, wanda ya shafe sama da watanni biyu ya jefa asibitocin gwamnati da kuma marasa lafiya cikin mummunann yana yi.

Sabon shugaban NARD, Godiya Ishaya, wanda ya tabbatar da janye yajin aikin, yace sun ɗauki matakin ne bayan taron kwamitin zartarwa na ƙungiyar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa

Lokita sanye da kayan aiki
Dalilin da yasa muka janye yajin aiki bayan shafe watanni biyu muna fafatawa, Lokitoci Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa janye yajin aikin zai soma aiki ne daga ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Laraba, lokacin da ake tsammanin kowane likita zai koma bakin aiki.

Meyasa suka janye yajin aikin?

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan taronta na ranar Lahadi, NARD tace ta ɗauki wannan matakin ne domin baiwa gwamnatin tarayya lokaci ta cika mata bukatunta.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa zata sake nazari kan lamarin bayan mako shida, wani sashin sanarwar yace:

"Bayan kula da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi kan dukkan abubuwan da suka jawo yajin aikin mu, an samu cigaba sosai daga FG wajen cika alkawurra."
"Kwamitin zartarwa NEC ya ɗauki matakin janye yajin aikin, wanda muka fara shi tun ranar 2 ga watan Augusta."
"Saboda haka, mambobin mu zasu koma bakin aiki daga ranar Laraba 6 ga watan Oktoba, da misalin ƙarfe 8:00 na safe."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Wannan sanarwa da NARD ta fitar tana ɗauke da sa hannun sabbin shugabanninta, Mista Ishaya, shugaban NARD, Sakatare Suleiman Ismail, da kuma sakataren watsa labarai, Alfa Yusuf.

A wani labarin kuma Asirin wasu masu satar mutane a tashar motoci ya tonu a jihar Kano

Gwarazan jami'an yan sanda sun cafke wata tawagar masu garkuwa da mutane dake gudanar da aikinsu a tashoshin mota.

Kakakin rundunar yan sanda ta ƙasa, Frank Mba, ya bayyana cewa jami'an sun kwato manyan makamai daga hannun mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel