Rikici yayin da dillalai suka ba mutane sama da 100 hayan gidaje 11 da dama akwai mutane

Rikici yayin da dillalai suka ba mutane sama da 100 hayan gidaje 11 da dama akwai mutane

  • Wani bidiyon mutanen da ke korafi game da damfararsu da dillalai suka yi kan hayan gidajen da dama akwai mutane a ciki ya yadu a duniya
  • A cikin bidiyon, duk sun ba da labarin yadda suka biya kudi a lokuta daban-daban sai kawai suka zo suka ga ashe an damfare su ne
  • Mutane da dama da suka mayar da martani kan faifan bidiyon sun ce ya kamata a yi maganin dillalan gidaje marasa gaskiya

Legas - Wani faifan bidiyo da ya nuna wasu mutanen da suka biya kudin hayan gidaje a unguwar Akoka da ke jihar Legas, ya jawo cece-kuce a yanar gizo.

Shafin Instagram na @instablog9ja da ya yada bidiyon ya bayyana cewa, sama da mutane 100 sun biya kudin hayan sabbin gidaje 11 da aka gina.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Masari ya bayyana mutanen da suka kashe kwamishina a Katsina

Bidiyon kwara rikicin dillai
Dillalai sun hada fada, sun ba mutane sama da 100 hayan gidaje 11 da akwai mutane | Hoto:@instablog9ja
Asali: Instagram

Gidaje 11, 'yan haya sama da dari

A cikin faifan bidiyon, wani mutum da ya biya sama da Naira 400,000 na wani karamin gida ya yi magana kan yadda ya hadu da wani wanda shi ma ya biya kudin gidan da ya biya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matashin ya ce dillalin da ya ba kudin hayan ya yi alkawarin cewa zai iya shiga gidan nan da mako na biyu na farkon watan Disamba.

Wasu mutanen da suka yi magana a cikin bidiyon sun ba da labarin yadda suka yi mamakin ganin cewa gidajen da suka biya hayar an riga an mamaye su.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

A lokacin rubuta wannan rahoto, faifan bidiyon ya tattara maganganun jama'a sama da 1,600.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikinsu kamar haka:

_aniscooser yace:

"Abinda wadannan mutane ke fuskanta bai kamata a dauke shi da wasa ba. Yana da matukar cin rai. Ina fatan za su shawo kan lamarin nan."

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

Wattsamos ya ce:

"Dillali ya yi amfani da kudinku ya gina gida ya gudu. Mafita kawai shine a rushe gidan."

cakes_nd_pops

"'Yan Najeriya da miyagu 5 da 6, mu ne matsalar mu."

lichy_com ya ce:

"Sun yi amfani da kudin su sun kammala gida."

johnarthur222 ya ce:

"Wayyo Allah wannan tsantsar mugunta ce."

Tufinplug ya ce:

"Waannan mutanen suna magana ba su san ainihin labarin ba, na biya tun wata 5 da suka wuce suna ci gaba da yin tura mu."

Bayan auren mata biyu masu juna biyu, ango ya ji dadin zama dasu, ya ce dole ya yi kari

A wani labarin, wani wanda ya auri mata biyu a rana guda mai suna Prince Erere Nana ya shawarci maza da su auri mata fiye da daya, matakin da ya ce zai dakile magudi a gidan aure.

Mutumin dan Najeriya daga kauyen Orhokpokpor da ke Delta ya jawo cece-kuce a intanet bayan sanar da gayyatar daurin aurensa inda ya bayyana cewa zai auri mata biyu masu juna biyu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Da yake magana a wajen rufe bikin aurensa na gargajiya da matansa, Erere ya shaida wa BBC News Pidgin cewa shi ne mutumin da ya fi kowa farin ciki a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel