Bayan auren mata biyu masu juna biyu, ango ya ji dadin zama dasu, ya ce dole ya yi kari

Bayan auren mata biyu masu juna biyu, ango ya ji dadin zama dasu, ya ce dole ya yi kari

  • Wani mutum dan jihar Delta mai suna Prince Erere Nana da ya auri mata biyu masu juna biyu a lokaci guda ya bayyana cewa shi ne mutumin da ya fi kowa farin ciki a duniya
  • Sabon angon duk da cewa ya auri mata biyu ya ce mai yiyuwa ne ya kara auro wata matar ta uku a nan gaba
  • A cewar angon, mutanen da suke da mata daya bai kamata ake kirga su a matsayin mutanen da ke da aure ba

Delta - Wani wanda ya auri mata biyu a rana guda mai suna Prince Erere Nana ya shawarci maza da su auri mata fiye da daya, matakin da ya ce zai dakile magudi a gidan aure.

Mutumin dan Najeriya daga kauyen Orhokpokpor da ke Delta ya jawo cece-kuce a intanet bayan sanar da gayyatar daurin aurensa inda ya bayyana cewa zai auri mata biyu masu juna biyu.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Ina Son Fatima, Ba Zan Fasa Auren Ta Ba, In Ji Saurayi Habib Suleiman Da Budurwarsa Ta Daɓa Wa Wuƙa

Mutumin da ya auri mata masu juna biyu
Bayan auren mata biyu masu ciki, ango ya ji dadin zama dasu, ya ce dole ya yi kari | Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook

Ya ce namiji mai mata daya bai ma yi aure ba

Da yake magana a wajen rufe bikin aurensa na gargajiya da matansa, Erere ya shaida wa BBC News Pidgin cewa shi ne mutumin da ya fi kowa farin ciki a duniya.

A cewarsa, mutanen da suka auri mata daya basu yi aure ba tukuna.

Da yake bayyana muhimmancin auren mace fiye da daya, ya ce idan mutum ya auri mata daya kuma ya aka samu da ‘yan uwa suka kawo ziyara a lokacin da matar bata gida, hakan zai haifar da matsala ga sosai.

Da yake buga misali da kansa a wannan yanayin, Erere ya ce shi da kansa ba zai iya dafa wa ’yan uwansa idan matarsa ba ta nan (idan ya auri mace daya) ganin cewa shi mutumin gargajiya ne.

Kara karanta wannan

Sarkin Sheɗanu: Fitaccen Mai Maganin Gargajiya Na Najeriya Mai Mata 59 Da ƳaƳa Fiye Da 300 Ya Mutu

Mutumin mai cike da farin ciki ya bayyana cewa mai yiwuwa zai auri mata ta uku, kalaman da amaren suka yi watsi da su a hirar da suka yi da juna.

Martanin jama'a

Abbanna Nneka ya ce:

"Abu mafi mahimmanci shine fahimta da dattaku a batun, jinjina ga matar farko, ina matukar kaunarki momma, ba kowace mace ce za ta iya yin haka ba, ina jinjina ma."

Antonia Nwakanma ya rubuta:

"Abin da kowa ke so a rayuwar nan farin ciki ne...tunda matan ka suna faranta maka rai shikenan hmmmm abeg carry dey goooo joor."

Oliseh Victor Dorgu Tombia ya ce:

“Mu mazan Delta da ke da mace daya ya za mu yi?, ko da muka auri mace daya, idanunmu har yanzu suna mana totori, Abeg ka taimake mu, mu ma muna son ’ya’ya da mata da yawa, har ma da yawan mu da aka haifa ba jihar Delta ba, har yanzu muna kokawa da wannan dabi'ar ta zama da mace daya a matsayin mata.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

"Ba zan iya cewa ka fara fada da ni ba, amma gaskiya nake fada, ka tambayi duk da aka haifa a cikin wannan gari na delta, jama'ar ijaw..."

Tijani Olabode ya ce:

“Dan uwa na bana adawa da ra’ayinka amma ka yi kokari ka kawo ‘ya’yanka don kada mu samu barayi a ko’ina ka auna shin kana iya kula da kan ka mata da ’ya’ya ba wai kawai ka ji dadin kanka ba don Allah ka duba kuma za ka iya tarbiyyantar da ’ya’ya nagari”.

Bidiyon matashi na tura wa 'yan NEPA karnuka yayin da suka zo yanke wuta

A wani labarin, wani faifan bidiyo na bidiyo ya nuna wani matashi da karnuka biyu yayin da ya tsare su daga tsorata jami'an NEPA.

Kafar Instagram ta @Instablog9ja da ta sake yada faifan bidiyon ta ce matashin ya yi amfani da karnuka wajen hana wasu jami’an NEPA gudanar da aikinsu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

A cikin faifan bidiyon, an ga karnukan sun yi kamar sun shirya tsaf don farmakan jami'an. Bayan mutumin kuwa, an ga wani tsani jingine a jikin pole din wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel