EFCC: Mun sake bankado $72.87m da Diezani ta boye a bankin Najeriya

EFCC: Mun sake bankado $72.87m da Diezani ta boye a bankin Najeriya

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sake bankado wasu $72.87 da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ta boye a wani fitaccen banki
  • Hukumar EFCC ta yi ram da manajan daraktan bankin na lokacin da Diezani ta rike kujerar ministar man fetur, Nnamdi Okonkwo
  • A lokacin mulkin Goodluck Jonathan, Madueke tana cikin masu fadi a ji, hakan ya ba ta damar wawurar dukiyar kasa tare da killacewa domin amfanin kan ta

Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta ce ta samo $72.87 miliyan da ke da alaka da tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke.

Hukumar EFCC ta tabbatar da hakan yayin sanar da kamen Nnamdi Okokwo, tsohon manajan daraktan fitaccen banki a Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

EFCC: Mun sake bankado $72.87m da Diezani ta boye a bankin Najeriya
EFCC: Mun sake bankado $72.87m da Diezani ta boye a bankin Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A baya, hukumar ta kama Okonkwo, wanda shi ne manajan daraktan bankin yayin da Madueke ke minista, Daily Trust ta ruwaito.

Tsohuwar ministar man fetur, wacce ta ke daga cikin masu karfin iko a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta shiga cikin sahun wadanda ake nema ido rufe kan zargin rashawa.

EFCC ta kwace kadarori masu tarin yawa wadanda aka gano ta same su ne ta hanyar da bata dace ba.

A wata takarda ta ranar Laraba, Wilson Uwujaren, kakakin EFCC, ya ce, "daga cikin ayyukanmu na bincike kan tsohuwar ministan man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta kama tsohon manajan banki, Nnamdi Okokwo, kan zargin samun karin $72, 870,000 miliyan a bankinsu," takardar tace.

"EFCC ta titsiye Okonkwo wanda a halin yanzu shi ne shugaban wani fitaccen banki, tare da wasu kan wasu kudi da suka kai $153 miliyan da $115 miliyan.
"EFCC ta samo dukkan $153 miliyan, a halin yanzu ana bincike kan $115 miliyan da suke da alaka da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
"A halin yanzu, Okonkwo da Charles Onyedibe suna garkame a hukumar EFCC domin son sanin inda kudin da aka bankado suke," ya kara da cewa.

Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske

A wani labari na daban, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya ce babu wasu rigunan mama da aka samo daga Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur, TheCable ta wallafa.

Diezani, wacce ta hanzarta barin kasar nan bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, an zarge ta da sace $2.5 biliyan daga gwamnatin tarayya yayin da ta ke minista, lamarin da ta musanta.

A watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta jero wasu kadarori da ta kwace daga Diezani wanda suka hada da tamfatsesen gida a Banana Island Foreshore Estate, Ikoyi, Lagos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel