Babbar magana: EFCC ta maka Fami Fani-Kayode a kotu bisa wasu laifuka 12

Babbar magana: EFCC ta maka Fami Fani-Kayode a kotu bisa wasu laifuka 12

  • Hukumar EFCC ta tasa keyar Fami Fani-Kayode zuwa kotu kan batun hada rahoton asibiti na bogi
  • A halin yanzu dai yana harabar kotu ana duba yiyuwar gurfanar dashi a gaban wacce ke zama a birnin Legas
  • Ana zargin Kayode a baya ya ba da takardun likita na bogi ne yayin da ake shari'a dashi kan wawure wasu kudade

Legas - Hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC a ranar Talata ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, a gaban kotun laifuffuka na musamman da ke Ikeja, kan zargin sa da yin takardun asibiti na bogi.

Ministan da ake cece-kuce akansa wanda dan jam’iyyar APC mai mulki ne, da misalin karfe 9 na safe jami’an EFCC suka kai shi gaban mai shari’a O.O Abike-Fadipe domin duba yiyuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

Femi Fani-Kayode
Yanzu-Yanzu: EFCC ta maka Fami Fani-Kayode a kotu saboda hada takardun bogi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A yanzu haka yana dakin kotun har zuwa lokacin hada wannan rahoto, inji jaridar Punch.

Hukumar ta EFCC ta yi ikirarin cewa Fani-Kayode ya sayi wani Dokta Ogieva Oziegbe domin ya bayar da rahoton likitan na bogi, wanda ake zargin ya gabatar a gaban babbar kotun tarayya a shari’ar da ake dashi na wawure wasu kudade.

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kotu bisa laifuka 12.

A wani bangare takardar tuhumar ta ce:

“Kai Femi Fani-Kayode a ranar 11 ga Oktoba, 2021 a Legas ko kuma a ranar 11 ga Oktoba, 2021 a gaban wannan kotun mai girma da nufin yaudarar babbar kotun tarayya da ke Legas mai lambar shari'a FHC/L. /251C/2016 ka kirkiri wata shaida ta karya mai suna: MEDICAL REPORT ON OLUFEM! FANI KAYODE 60 YEARS/MALE/HOSP. NO.00345 DATED 11/10/2021 kuma ana zargin cewa babban asibitin Kubwa ne ya bayar."

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya fallasa dabarun Alkalai, ya bayyana yadda suke samun kudin haram

An yi nuni da cewa laifin ya sabawa doka kuma yana daukar hukunci ne a karkashin sashe na 88(1) (a) na dokar laifuka ta jihar Legas 2015.

Fani-Kayode dai ya dade yana fafatawa da hukumar EFCC kuma an taba tsare shi na tsawon kwanaki 67 a shekarar 2016 tare da tsohon ministan kudi, Nevada Usman.

Mutanen biyu da wasu biyu daban suna fuskantar tuhume-tuhume 17 da suka hada da hada baki, zamba da kuma karkatar da kudaden da suka kai Naira biliyan 4.9.

Sun musanta zargin, kuma daga baya an bayar da belin kowannen su akan Naira miliyan 250.

Da yake bayyana a gaban kotun, Lauyan hukumar EFCC, Mista Rotimi Oyedepo, ya roki kotun da ta duba yiyuwar hukunta wanda ake kara kan zargin, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Sai dai lauyan wanda ake kara, Mista Wale Balogun, ya ki amincewa da bukatar EFCC, ya ce tawagar masu kare Kayode sun shigar da kara domin kalubalantar hurumin kotun don duba lamarin.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Da yake mayar da martani, Mista Oyedepo ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar bisa hujjar cewa wani yunkuri ne na kawo cikas ga shari’ar saboda ana tuhumar wanda ake tuhuma ne da shari’ar Legas kuma ba za a iya sauraron karar ba sai dai a Legas.

Biyo bayan shawarwarin lauyoyi da kuma gabatar da jawabai, Mai shari’a Abike-Fadipe ta tsayar da ranar 17 ga Disamba, 2021, don yanke hukunci kan bukatarsu.

Jami'an hukumar EFCC sun damke tsohon minista Fani-Kayode

A baya kunji cewa, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya shiga hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) a jihar Legas.

Punch ta rahoto cewa tsohon ministan na karkashin binciken hukumar ne bisa zargin amfani da jabun takardu da kuma magudi.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an EFCC sun kai tsohon minista Kayode ofishinsu na jihar Legas ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel