Daga karshe: Gwamnati ta tona asirin kungiyoyin da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Daga karshe: Gwamnati ta tona asirin kungiyoyin da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

  • Mai ba Buhari shawari kan harkokin tsaro ya bayyana sunayen kungiyoyin da ke daukar nauyin ta'addanci
  • Ya bayyana neman goyon bayansa ga malaman addinin Islama a yaki da ake yi da ta'addanci a wannan lokaci
  • Ya kuma yi kira da hadin kai da goyon bayan shugabannin al'umma domin kawo karshen wannan ta'addanci

Abuja - Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd), ya bayyana sunayen kungiyon da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya da sauran kasashen Sahel.

A cewarsa, Jama'at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS sune kunyoyin da ke karfafa ayyukan ta'addanci, The Nation ta ruwaito.

Mai ba shugaba Buhari shawari kan harkokin tsaro, Babagana Munguno
Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta bayyana kungiyoyin da ke daukar nauyin ta'addanci | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Munguno ya bukaci masu wa'azin addinin Islama da Limamai da su dauki matsaya mai kyau don tallafawa ayyukan gwamnati a yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sace mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamna a Arewa

Ya lura cewa kawance tsakanin malamai da jami'an tsaro "ya zama kashin bayan sake gina al'ummominmu da ta'addanci suka mamaye".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Munguno ya yi wannan jawabi ne a wajen taron karawa juna sani na kungiyar Malamai da masu wa’azi da limaman kasashen Sahel karo na 14 a Abuja.

Yace:

"Ta'addanci da karuwar ayyukan ta'addanci daga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin Islama a yankin Sahel tun daga shekarar 2016, kungiyar Islamic State in Greater Sahara (ISGS) ce ke jagorantarsu, wadda galibi ke aiki a Mali har zuwa Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.
“Ayyukan kungiyoyi irin su Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS, ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar yankin.
“A Najeriya, kungiyar Boko-Haram da kungiyar Islamic State of West African Province (ISWAP) ne suka mamaye ayyukan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

“Halin da ake ciki a yankin Sahel bai taba yin muni kamar yanzu ba, tashe-tashen hankula na ci gaba da yaduwa; Adadin mutanen da ke gudun hijira (IDPS) na karuwa; kuma karancin abinci yana shafar mutane fiye da kowane lokaci.
"Akwai wasu jita-jita da ba su dace ba da ke karfafa dabarun gwamnatocin kasashen waje da na yankin".

Munguno ya kara da cewa:

"Yana da matukar muhimmanci a sake tantancewa da kuma sake tsara dabarun da za a bi a yankin Sahel, tare da ajiye zato mara kyau.

Da yake jan hakalin malaman addinin Islama, The Guardian ta ruwaito Munguno na cewa:

“A dangane da haka, ya zama wajibi malamai, masu wa'azi da shugabannin al’umma na yankunanku su ba da gudummawa wajen tallafa wa kokarin jami’an tsaronmu, domin kawo karshen wannan matsala.
"Kamar yadda hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci ke kara habaka ci gaban jami’an tsaro a fagen yaki da ta’addanci, ya kamata kawance da kokarin kungiya irin na LOPIS su zama kashin bayan sake gina al’ummarmu da ta’addanci ya mamaye.

Kara karanta wannan

Kungiyar IZALA ta bada umarnin fara Alkunut a masallatan Ahlissunnah dake fadin Najeriya

"Babu wata bindiga da ta fi karfin wayewa da ilimi a matakin tushe.”

Rahoto: Dalla-dalla kisan mutane 3,125, da sace 2,703 a cikin watanni 11 a Arewa

A baya kunji cewa, a wani abin da zai ci gaba da ba wa ‘yan Najeriya bakin ciki, wani rahoto ya nuna cewa akalla mutane 3,125 ne ‘yan bindiga suka kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, tare da yin garkuwa da 2,703 a arewacin Najeriya a cikin watanni 11 da suka wuce.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an samu wadannan alkaluman ne daga wani shiri na hukumar kula da harkokin kasashen waje ta Amurka mai suna Nigeria Security Tracker.

Ya kuma kara da cewa rahoton yace an tattaro daga rahoton kwata-kwata da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar daga watan Janairu zuwa Satumba.

Jihohin da lamarin ya fi shafa sun hada da Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina, Neja da Borno.

Kara karanta wannan

Kasashen musulman duniya sun yi Allah-wadai da babbaka matafiya a Sokoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel