Da Ɗumi-Ɗumi: An sace mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamna a Arewa

Da Ɗumi-Ɗumi: An sace mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamna a Arewa

  • Miyagun 'yan bindiga sun sace Madam Seriya Raji, mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
  • Makwabtan Seriya Raji sun ce lamarin ya faru ne a daren jiya inda yan bindiga suka kutsa gidanta ta cikin masallacin da ke jikin gidan suka sace ta
  • A cikin makonni da suka gabata, 'yan bindiga sun kai wa kwamishinan muhalli na jihar Kogi, Adewale Omofaiye hari amma ba su yi nasara ba

Kogi - Makonni kadan bayan Kwamishinan Muhalli na Jihar Kogi, Adewale Omofaiye, ya tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwa, 'yan bindiga sun sace mahaifiyar Abdulkarim Jamiu Asuku, shugaban ma'aikatan fadar Gwamna Yahaya Bello.

SaharaReporters ta ruwaito cewa majiyoyi sun bayyana cewa an sace Madam Seriya Raji ne misalin karfe 8 na daren ranar Litinin a gidan ta da ke yankin Nagazi da ke Okene a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

Da Ɗumi-Ɗumi: An sace mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamna a Arewa
An sace mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamnan Kogi. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya faru

Yan bindigan, wadanda suka saka takunkumin fuska sanye da bakaken tufafi, sun kutsa dakinta ne ta cikin masallaci da ke jikin gidanta, a cewar daya daga cikin makwabtanta.

A halin yanzu ba su tuntubi iyalanta ba ko wani na kusa da ita domin neman kudin fansa, Daily Trust ta ruwaito.

William Aya, mai magana da yawun yan sandan jihar Kogi, bai amsa kirar da aka masa ba da sakon kar ta kwana a lokacin hada wannan rahoton.

A makon karshe na watan Nuwamba, an kai wa Kwamishinan Kogi, Omofaiye, hari a tsakanin Ikoyi da Iyara a jihar inda ya tsira da raunuka.

An ruwaito cewa mutane uku ne ke cikin motan a lokacin da miyagun da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai musu harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10

SaharaReporters ta ruwaito cewa mutanen da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun bude wa motarsa wuta a yayin da ya ke hanyarsa ta zuwa Lokoja inda suke harbe shi a kafarsa.

An ruwaito cewa an sace wasu masu ababen hawa a titin sannan aka yi cikin daji da su.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel