Da Duminsa: Dan takarar gwamna ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota

Da Duminsa: Dan takarar gwamna ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota

  • Wani dan takarar gwamna a jihar Benue ya yi hatsari, inda aka ce ya ji karamin rauni a kai yayin hatsarin
  • Rahoto ya bayyana cewa, motar dan takarar gwamnan ta yi karo ne da wata motar kasuwanci, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wani
  • A halin yanzu dai ance an kai dan takarar gwamnan asibiti tare da direban da sauran wasu mutane da suka jikata

Benue - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wani dan takarar gwamna kuma tsohon shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Benue, Terwase Orbunde a ranar Litinin ya tsallake rijiya da baya.

Majiyoyi sun ce motar Orbunde ta yi mummunan hatsari a kauyen Uchi da ke kan titin Makurdi/Gboko.

Orbunde shi ne shugaban ma’aikatan gwamna Ortom amma ya yi murabus a watan Satumba domin cimma burinsa na tsayawa takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sace mahaifiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamna a Arewa

Taswirar jihar Benue
Dan takarar gwamna ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani mawallafi, Babs Usigbe da shaida hatsarin ya ce dan takarar gwamnan ya samu dan rauni a kai.

An ce Orbunde yana dawowa ne daga wurin bikin yin murabus dinshi a Gboko da misalin karfe 5:00 na yamma lokacin da hatsarin ya afku.

A cewar Usigbe, ganau a lokacin hatsarin:

“Ina kan hanyata daga Katsina Ala zuwa Gboko na dawo Makurdi lokacin da na ga hatsarin.
“Wata motar kasuwa da ta taho daga Makurdi ta yi aron hanya a mike. Maimakon direban motar ya koma hannunsa, sai ya fuskanci motar da mai neman kujerar gwamnan ke cikinta, ya buga ta da jikin bishiya.
"Orbunde ya samu dan rauni a kai amma daya daga cikin fasinjojin motar kasuwar ya mutu nan take yayin da wasu fasinjoji takwas suka samu munanan raunuka."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamna ya kori kwamishinan lafiya saboda yi masa katsalandan

Shaidan ya ce an garzaya da dan takarar gwamnan da direbansa da kuma wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba.

Da yake tabbatar da faruwar hatsarin, kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Benu, Yakubu Mohammed ya ce mutum daya ya mutu a hatsarin amma ya kara da cewa har yanzu bai samu cikakken bayani ba.

A cewar Mohammed:

“Gaskiya ne an yi hatsarin mota amma har yanzu ban samu cikakken bayani kan hatsarin ba. Duk da haka, zan iya tabbatar da cewa mutum daya ya mutu."

Kokarin neman abokin dan takarar gwamnan kan harkokin yada labarai, Tahav Agerzua bai yi nasara ba saboda bai dauki kiran da aka yi masa a wayar salula ba.

Gwamna ya kori kwamishinan lafiya saboda yi masa katsalandan

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kori kwamishinansa na ma'aikatar lafiya, Farfesa Princewill Chike, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai

Gwamna Wike ya bayyana hakan ne a zauren majalisar zartarwa ta Jiha a ranar Litinin yayin wata ziyarar ban girma da jami’an kungiyar likitoci ta Najeriya suka je gidan gwamnati domin yi masa bayani kan taron kasa da suka gudanar a Fatakwal.

Gwamnan ya fusata cewa korarren kwamishinan ya amince da gudanar da taron kawai ba tare da bin ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel