Yadda shugaban dakarun Abacha, Manjo Al'mustapha, ya cece ni daga Fyade, Hadimar Buhari

Yadda shugaban dakarun Abacha, Manjo Al'mustapha, ya cece ni daga Fyade, Hadimar Buhari

  • Kafin ta zama shugaban hukumar NIDCOM, Abike Dabiri ta rike mukamin babbar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin kasashen waje
  • Dabiri ta bayyana yadda ta shiga kalubale har aka kamata lokacin tana aikin jarida, kuma Manjo Al-Mustapha ya tserad da ita daga fyade
  • Tace akwai bukatar a baiwa yan jarida kariya, kuma ya kamata su cire tsoron komai daga zukatan su

Abuja - Shugaban hukumar yan Najeriya dake kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana irin kalubalen da ta shiga ta yadda aka kusa mata fyaɗe lokacin da take aikin jarida.

Dailytrust ta rahoto cewa Abike Dibiri ta faɗi haka ne yayin da take jawabi ga manema labarai bayan karban lambar girmamawa a wurin taron yancin neman bayanai (NFI) a Abuja.

Tsohuwar yar majalisar tarayya ta shaidawa yan jarida su tashi tsaye kuma su ƙarfafa kansu, su rinka gudanar da binciken kwakkwafi kan wani abu.

Abike Dibiri
Yadda shugaban dakarun Abacha, Manjo Al'mustapha, ya cece ni daga Fyade, Hadimar Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta kara da cewa ba dan Manjo Janar Al-mustapha, tsohon shugaban dakarun marigayi shugaban ƙasa, Janar Sani Bacha, ya shiga ciki ba, da an mata fyaɗe a wancan lokacin.

Abike ta yi kira ga yan jarida kada su ji tsoron shiga ko ina ne su gudanar da binciken kwakkwafi kan masu rike da madafun iko.

Tace:

"Duk mai nema yana tare da samu, na shiga hannu a dai-dai lokacin nake gudanar da binciken aikin jarida, an rufe ni a Apapa, ɗaya daga cikin sansanin sojoji."
"Mejo Hamza Al-Mustapha, shine ya tseratad da ni daga yi mun fyaɗe, ya zo a lokacin da ya dace. Dan haka kada kuji tsoron komai."

Ta kuma kara da cewa akwai bukatar tabbatarwa da kare rayuwar yan jarida domin su samu damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Muƙaman da ta taba rike wa

Dabiri ta yi aiki a kafar watsa labarai ta ƙasa (NTA) na tsawon shekara 15, tana gudanar da shirin labarai na NTA News Line.

Ta yi ritaya daga aiki a NTA kuma ta nemi takarar yar majalisar wakilan tarayya, inda bayan zaɓe ta samu nasara.

A shekarar 2015, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa ta babban mai bashi shawara kan harkokin yan Najeriya dake kasashen waje.

Bayan shekara uku, Buhari ya maida ta shugabar hukumar NIDCOM, matsayin da take rike da shi har zuwa yau, kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito.

A wani labbarin kuma Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar ASUU

Gwamnatin tarayya ta fara cika alkawurran da ta ɗaukarwa kungiyar malaman jami'o'i ASUU kafin ta janye yajin aiki a baya.

Ministan kwadugo, Chris Ngige, yace tunin gwamnati ta tura wa jami'o'i kudin gyara da alawus kimanin biliyan N55.2bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel