Zamu share yan bindiga daga doron ƙasa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnan Sokoto

Zamu share yan bindiga daga doron ƙasa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnan Sokoto

  • Tawagar da shugaban ƙasa ya tura ta kai ziyarar jaje da ta'aziyya ga gwamnatin Sokoto da al'ummar jihar baki ɗaya
  • Shugaba Buhari ya jaddada kokarin gwamnatinsa na kawo karshen ayyukan yan bindiga a faɗin kasar nan
  • Ya umarci dukkan hukumomin tsaro su tabbata sun kamo duk masu hannu a wannan kisan na rashin tausayi

Sokoto - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na magance yan bindiga domin kare yan Najeriya daga sharrin su.

Buhari ya yi wannan furucin ne lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyarar jaje ga gwamna Aminu Tambuwal bisa kisan matafiya 23 a jihar Sokoto.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin gwamnan Sokoto, Muhammad Bello, ya fitar ranar Asabar, kamar yadda daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tabbas jam'iyyar PDP zata sake lashe jihohi akalla 25 a zaben 2023, inji Ayu

Shugaba Buhari
Zamu share yan bindiga daga doron ƙasa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnan Sokoto Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban tawagar gwamnatin tarayya kuma mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, shine ya isar da sakon shugaban ƙasa na jaje da ta'aziyya.

Buhari ya yaba wa gwamna Tambuwal bisa datse tafiyar aiki da ya yi domin karɓan tawagar gwamnatin tarayya duk da ba'a sanar masa a kan lokaci ba.

Guardian ta rahoto shi yace:

"Mun zo Sokoto bisa umarnin shugaba Buhari, dan jajanta maka da sauran al'umman Sokoto da kuma mai martaba sarkin Musulmi, kan abubuwa mara daɗi dake ta faruwa a makonnin da suka shuɗe."
"Shugaban ƙasa ya damu sosai kan yadda ake samun faruwar haka lokaci bayan lokaci, wanda ke sanadin rasa rayuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba."
"Kowane rai na da muhimmanci, abun na damun shugaban ƙasa yadda mutane ke mutuwa ta hanyar rashin tausayi. Shugaba Buhari na mika ta'aziyyarsa kan yan Najeriya da suka mutu."

Kara karanta wannan

Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa, EFCC ta magantu

Wajibi a hukunta masu hannu a kisan matafiya - Buhari

Monguno ya ƙara da cewa, shugaba Buhari ya jaddada kokarin gwamnatinsa na tabbatar da an kame duk mai hannu a kisan kuma sun girbi abinda suka shuka.

"Buhari ya ƙara jajanta lamarin tare da tabbatar da cewa an cafke duk me alaƙa da wannan kisan na rashin Imani da rashin tausayi kuma a hukunta su."
"Shugaban ƙasa ba ya jin daɗin halin da yan ƙasa suka tsinci kansu, ya umarci dukkan hukumomin tsaro kada su huta har sai sun share baki ɗaya waɗan nan yan ta'addan."
"Dukkan hafsoshin tsaro suna nan, wanda hakan wata alama ce shugaban ƙasa na kokarin shawo kan wannan lamarin."

Yan bindiga na shigowa daga Zamfara - Tambuwal

Da yake nasa jawabin, Gwamna Tambuwal yace a kwanan nan yan bindiga da masu garkuwa sun jefa al'ummar Sokoto cikin mawuyacin hali.

A cewar gwamnan, luguden wutan dakarun soji na Operation Hadarin Daji a Sokoto don kawo karshen yan bindiga a Zamfara, shi ke koro su zuwa Sokoto.

Kara karanta wannan

Yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya tserad da ni daga yi mun fyade, Hadimar Buhari

A wani labarin na daban kuma Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar ASUU

Gwamnatin tarayya ta fara cika alkawurran da ta ɗaukarwa kungiyar malaman jami'o'i ASUU kafin ta janye yajin aiki a baya.

Ministan kwadugo, Chris Ngige, yace tunin gwamnati ta tura wa jami'o'i kudin gyara da alawus kimanin biliyan N55.2bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel