Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar ASUU

Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar ASUU

  • Gwamnatin tarayya ta fara cika alkawurran da ta ɗaukarwa kungiyar malaman jami'o'i ASUU kafin ta janye yajin aiki a baya
  • Ministan kwadugo, Chris Ngige, yace tunin gwamnati ta tura wa jami'o'i kudin gyara da alawus kimanin biliyan N55.2bn
  • Yace aiki yayi nisa a kan gwaji da bincike na tsarin biyan albashi UTAS da ASUU ta gabatar wa FG

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta tura wa malaman jami'o'i biliyan N30bn na gyara da biliyan N22.5 na alawus kuma ta yi nisa wajen cika sauran yarjejeniyar (MoU) da aka cimma.

Ministan kwadugo, Chris Ngige, shine ya bayyana haka ga This Day, yayin da yake jawabi kan halin da ake ciki gmae da kungiyar ASUU.

Ministan yace ya samu bayanai daga ma'aikatar kudi cewa an tura kudin ga jami'o'in domin gyara da kuma alawus ɗin malamai.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An damke Diraktan ma'aikata a jihar Kano yana tsakiyar karbar cin hanci

Ngige
Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar ASUU Hoto: dailpost.ng
Asali: UGC

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jiya Jumu'a, ofishin Akanta Janar da ofishin kudi na ma'aikatar kudi da kasafi, sun faɗa mun cewa an tura kudin alawus ga jami'o'in gwamnatin tarayya 38, kuma zuwa yau (Asabar) dukka waɗan nan jami'o'in zasu samu kuɗin su."
"Kuma tuni na tura wa shugabannin ASUU halin da ake ciki domin su sani."

Mun kammala bincike a kan UTAS - Ngige

Dakta Ngige ya kara da cewa gwamnati ta kammala bincike kan lamarin da ya shafi sabon tsarin biyan albashi na UTAS wanda ASUU ta gabatar mata.

"Yau ɗin nan da muke ciki hukumar fasaha (NITDA) ta mika rahoton binciken da ta gudanar kan UTAS, kuma tuni aka turawa ma'aikatar kudi, ofishin Akanta Janar da ofishin IPPIS domin su duba."
"Sannan kuma an tura kwafin wannan rahoto ga ma'aikatar ilimi da kuma hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC)."

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

Ministan ya bayyana cewa UTAS ya samu kaso sama da 50 a makin da aka yi amfani da shi wajen gwaji da bincike, amma ya kara da cewa hukumomi na cigaba da aiki akansa.

A wani labarin kuma Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata

Jami'ar jihar Kwara (KWASU) ta sallami wani malami, Pelumi Adewale, bisa zargin da ake masa na neman ɗalibai da lalata.

Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran ya yi wa wata ɗaliba barazanar kada ita a kwas ɗin da yake ɗauka idan bata amince masa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel