Hare-haren Sokoto: Duk laifin Jami'an Sojojin Najeriya ne, Gwamna Tambuwal

Hare-haren Sokoto: Duk laifin Jami'an Sojojin Najeriya ne, Gwamna Tambuwal

  • Gwama Tambuwal ya karbi bakuncin tawagar da Shugaba Muhammadu Buhari ya tura ta musamman kai gaisuwar ta'aziyya Sokoto
  • Gwamnan ya bayyana ainihin abinda ya tsananta matsalar tsaro a jiharsa
  • Mota mai dauke Akala mutum 42 yan bindiga suka kona kurmus a jihar Sokoto farkon makon nan

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa shigowar yan bindiga jiharsa daga jihar Zamfara duk laifin jami'an Sojojin Najeriya ne.

Tambuwal ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wakilan Shugaban kasa da suka kai ziyarar jaje jihar Sokoto, rahoton Daily Trust.

A cewarsa:

"Atisayen Operation Hadarin Daji ne ya harzuka rikicin yan bindiga a Sokoto saboda an kora yan bindigan ba tare da taresu daga shiga sauran jihohi ba, irinsu Sokoto."

Kara karanta wannan

Shugabar Makaranta ta hana dalibai mata 2 zana jarabawa, tace sai sun cire Hijabi

"Kuma lokacin da akayi harin, jami'an tsaron basu da isasshen kayan aikin da zasu dakile yan bindigan da zasu shiga Sokoto."
"Abin dai tamkar an kori yan bindigan daga Zamfara sun koma Sokoto. Wannan abin tashin hankali ne."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Akwai bukatar a kara yawan Sojoji."

Gwamna Tambuwal
Hare-haren Sokoto: Duk laifin Jami'an Sojojin Najeriya ne, Gwamna Tambuwal Hoto: NASS
Asali: Depositphotos

Shugaba Buhari ba zai je Sokoto ba, amma ya tura IGP, NSA wakilci

Shugaba Muhammad Buhari, a ranar Juma’a ya tura wakilai jihar Sokoto da Katsina bisa rashin rayukan da akayi kwanaki biyu da suka gabata sakamakon hare-haren yan bindiga.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma’a.

Ya yiwa jawabin taken ‘Shugaba Buhari ya tura Shugabannin tsaro da na leken asiri Sokoto da Katsina’.

Wadanda Buhari ya tura sun hada da NSA, Major General Babagana Munguno; IG na yan sanda, Usman Alkali Baba; Dirakta Janar na DSS, Yusuf Magaji Bichi; Dirakta Janar na NIA, Ahmed Rufa’i Abubakar, da Shugaban leken asirin Soji, Major General Samuel Adebayo. I .

Asali: Legit.ng

Online view pixel