Shugabar Makaranta ta hana dalibai mata 2 zana jarabawa, tace sai sun cire Hijabi

Shugabar Makaranta ta hana dalibai mata 2 zana jarabawa, tace sai sun cire Hijabi

  • Duk da hukuncin kotu, wata shugabar makaranta a Legas ta hana dalibai mata Musulmai zana jarabawa
  • Mrs Odushoga ya bayyana cewa ba zasu bari wata daliba ta shiga musu makaranta sanye da Hijabi ba
  • Gwamnatin jihar ta baiwa kowace daliba damar sanya Hijabi kamar yadda addinita ya tanada

Legas - An hana daliban makarantar sakandaren Igboye dake garin Epe, jihar Legas biyu zana jarabawa saboda suna sanye da Hijabi.

Hakazalika an hanasu shiga makaranta makon da ya gabata yayinda ake shirin jarabawar.

Mahaifin daliban ya ziyarci makarantar inda ya nunawa Shugaban makarantar Mrs Odushoga hukuncin kotu da aka halaltawa dalibai sanya kayan addininsu.

Amma Shugabar makarantar ta lashi takobin cewa ba za'a barsu su zana jarabawa ba sa sun cire Hijabi, Kungiyar kare hakkin masu sanya Hijabi watau Hijab Right Advocacy Initiative ta bayyana a jawabi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An damke Diraktan ma'aikata a jihar Kano yana tsakiyar karbar cin hanci

Shugabar Makarantar
Shugabar Makaranta ta hana dalibai mata 2 zana jarabawa, tace sai sun cire Hijabi
Asali: Facebook

Jaridar Muslimnews ta ruwaito Shugabar kungiyar, Mutiat Orolu-Balogun, da cewa:

"An ce kowani yaro na da hakkin samun ilimi, amma an gaza baiwa dalibai Mata Musulami nasu hakkin."
"Mun aike sako wa Kwamishanar (jihar) kan wannan lamari ranar 8 ga Disamba, don gudu wannan rikicin."
"Hakazalika mun tattauna da ita kuma ta yi alkawarin dubi cikin lamarin. Mun kai kara kotu amma har yanzu wannan abu na faruwa da 'yayanmu."

An tada hayaniya bayan wani farfesa a LAUTECH ya tuɓe wa wata ɗaliba hijabi a bainar jama'a

Akwai yiwuwar rikici ya barke a Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, LAUTECH, da ke Ogbomoso, a ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba idan ba a dauki matakan dakile rikicin ba.

Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Ridwan Kolawole, ya bayyana cewa wasu kungiyoyin musulmi sun yi zanga-zanga kan abin da suka kira wuce gona da iri da Shugaban tsangayar Koyon Aikin Malaman Jinya, Farfesa Ajibade Lawal ya yi inda ya umurci wata daliba musulmi ta cire hijabi a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Ba zan bar masu hannu a kisan dalibin kwalejin Dowen, Oromoni, su ci bulus ba, Shugaba Buhari

Farfesa Lawal yana yi wa daliban tsangayarsa jawabi ne yayin wani taro na bude sashin koyarwa daga gida na LAUTECH tare da daliban tsangayar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel