Shugaba Buhari ba zai je Sokoto ba, amma ya tura IGP, NSA wakilci

Shugaba Buhari ba zai je Sokoto ba, amma ya tura IGP, NSA wakilci

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya tura tawaga ta musamman ka gaisuwar ta'aziyya Katsina da Sokoto
  • Kusan dukkan manyan shugabannin tsaro a Najeriya na cikin wannan tawaga ta musamman

Shugaba Muhammad Buhari, a ranar Juma’a ya tura wakilai jihar Sokoto da Katsina bisa rashin rayukan da akayi kwanaki biyu da suka gabata sakamakon hare-haren yan bindiga.

Wannan ya biyo bayan ziyarar da Shugaban kasan ya kai jihar Legas ranar Alhamis.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma’a.

Ya yiwa jawabin taken ‘Shugaba Buhari ya tura Shugabannin tsaro da na leken asiri Sokoto da Katsina’.

Shugaba Buhari ba zai je Sokoto ba, amma ya tura IGP, NSA wakilci
Shugaba Buhari ba zai je Sokoto ba, amma ya tura IGP, NSA wakilci
Asali: Depositphotos

A cewarsa,

“Shugaban kasa na jiran rahoton bincike da shawari kafin ya dau matakin magance lamarin.”

Wadanda Buhari ya tura sun hada da NSA, Major General Babagana Munguno; IG na yan sanda, Usman Alkali Baba; Dirakta Janar na DSS, Yusuf Magaji Bichi; Dirakta Janar na NIA, Ahmed Rufa’i Abubakar, da Shugaban leken asirin Soji, Major General Samuel Adebayo. I .

An yi jana'izar Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina da aka kashe a gidansa

An gudanar Sallar Jana'izar Kwamishsnan Kimiya da Fasahan jihar Katsina, Dr Nasir Rabe, karkashin jagorancin Limamin Masallacin Katsina GRA, Dr Aminu Abdullahi Yammawa.

An bizne marigayin ne a makabartan Gidan Dawa bayan Sallar Jana'izar, rahoto DailyTrust.

Shugaban tawagar Gwamnatin tarayya yace Shugaban kasa ne ya tura shi jajantawa Gwamnatin jihar Katsina da iyalan mamacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel