Maza sun kwanta: An gudanar da jana'izar Janar Wushishi a Sultan Bello dake Kaduna

Maza sun kwanta: An gudanar da jana'izar Janar Wushishi a Sultan Bello dake Kaduna

  • Tsohon hafsan rundunar sojojin kasan Najeriya, Janar Inuwa Wushishi, ya kwanta dama bayan fama da jinya a Landan
  • A ranar Laraba da muke ciki aka gudanar da jana'izar marigayin a babban masallacin Jumu'a na Sultan Bello dake Kaduna
  • Janar Abdulsalami Abubakar, ya yabi marigayin, tare da masa addu'a Allah ya gafarta masa yasa shi cikin gidan Aljanna

Kaduna - Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa a ranar Laraba, an gudanar da jana'izar tsohon hafsan rundunar sojin kasa, Janar Inuwa Wushishi a Kaduna.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta bayyana cewa an yi wa marigayin sallar jana'iza ne a babban masallacin Jumu'a na Sultan Bello.

Rahoton ya kuma kara da cewa bayan kammala sallar jana'lza kamar yadda addinin musulunci ya tanada, an binne gawarsa a makabartan Unguwan Sarki.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

Janar Wushishi
Maza sun kwanta: An gudanar da jana'izar Janar Wushishi a Sultan Bello dake Kaduna Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Janar Wushishi ya rasu ne a birnin Landan bayan fama da doguwar rashin lafiya, ya rasu yana da shekara 81 a duniya.

Manyan mutanen da suka halarci jana'iza

Daga cikin manyan sanannun mutanen da suka halarci jana'izan, akwai tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar.

Sauran sun haɗa da ministan tsaro, Bashir Magashi, da kuma shugaban rundunar sojin ƙasa na yanzu, COAS Farouk Yahaya.

Da yake jawabi ga manema labarai a gidan mamacin, Janar Abdulsalami ya bayyana marigayi Wushishi a matsayin, "Ɗan uwansa" da kuma mutum wanda ya gudanar da rayuwa abun koyi.

Haka nan kuma yace marigayin jami'i ne nagari mai sadaukar da kansa ga ƙasa, kuma dattijo ne wanda ya yi wa Najeriya aiki tukuru.

Kara karanta wannan

Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa mai tsada ranar daurin aurensu

Abdulsalami Abubakar ya nuna tsantsar damuwa da jimamin wannan babban rashi, inda ya yi Addu'a Allah yasa aljanna ta zama makoma a gare shi.

A wani labarin na daban kuma Wani barawo da dubunsa ta cika a Kano ya bayyana cewa har matansa na aure sun guje shi saboda sata

Uzairu, ɗan asalin garin Dayi a jihar Katsina , ya shiga komar yan sanda ne a wani Banki yayin da ya yi kokarin sace wani mashin kirar Suzuki.

Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, yace zasu gudanar da bincike kuma su mika shi ga kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel