Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

  • Prince Ned Nwoko a wata takarda da ya fitar ya bayyana dalilan da su ka janyo rabuwar aurensa da Laila, tsohuwar matarsa ‘yar kasar Morocco
  • Fitaccen dan kasuwar ya yi karin bayani akan asalin yadda lamarin ya auku inda ya ce ba gaskiya bane maganar Jaruma mai kayan mata wacce tace kayan ta ne su ka yi aiki
  • Ned Nwoko ya zargi Laila da rashin kamun kai tare da lallabawa wurin likita don a gyara mata halittarta ba tare da saninsa ba da kuma cutar da yaransa

Attajirin dan kasuwa kuma miji ga Regina Daniels, Prince Ned Nwoko, ta hanyar masu yada labaransa ya saki wata takarda wacce ya bayyana asalin abinda ya kawo karshen aurensa da matarsa ‘yar kasar Morocco, Laila.

A shafinsa na Instagram, ya fara da musanta ikirarin Jaruma Empire, mai sayar da kayan mata akan cewa kayan matanta ne suka janyo Ned ya rabu da Laila, kuma wannan maganar ta ta soki burutsu ce, karatun tsuntsaye.

Kara karanta wannan

Hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta bi don magance matsalolin tsaro, DSS

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko
Ned Nwoko ya bayyana abin da ya yi sanadin rabuwarsa da matarsa yar kasar Morocco, Laila: Photo: @princenednwoko
Asali: Instagram

Kamar yadda takardar tasa ta zo:

“A duba tarihi tukunna. Jaruma ta auri wani matashi mai karancin shekaru, ya aka yi auren bai wuce shekara daya ba, bayan haihuwar yaro daya? Ya aka yi kayanmatan bai tsayar da mijin ba?.”

Abinda ya janyo rabuwar auren Nwoko da Laila

A wani bangare na wallafar, ya kara da cewa aurensu ya rabu da Laila ne sakamakon wata sheke aya da ta yi lokacin da ta je hutu London.

An zargi Laila da kashe wa kanta kudin da ya kamata ta yi wa yara amfani da su wanda mijinta ya bayar.

Har ila yau, ya zargi Laila da zuwa wurin likita don inganta halittarta ba tare da saninsa ba sannan ta garzaya gidan rawa inda ta kwaso cutar Coronavirus.

Kara karanta wannan

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

A watan Augustan 2020, Nwoko ya zargi Laila da yin tafiyarta yayin da ta bar yara a dakin otal wanda ya ja su ka tafka barna mai yawa.

Kamar yadda takardar ta zo:

“Sai da ya kashe 7000 pounds saboda tsabar barnar da yara suka tafka a dakin otal din kafin a barsu su kwashe kayansu daga cikin dakin. Daga nan su ka koma wani otal din wanda ya janyo wa Ned Nwoko wata asarar.”

Sannan ya zargeta da dukan yaransu bayan sun sanar da mahaifinta irin ayar da ta dinga shekawa a London.

Ana zargin Laila da lalata da wani mutum

A wata takardar Nwoko ya zargi tsohuwar matarsa da sheke ayarta da wani. An zargeta da kulla alakar da wani a watan Janairun 2021.

An gano hakan ne yayin da ta je London a watan Augusta inda su ka dinga fita yawon shakatawa tare.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

Kara karanta wannan

An kama wani soja da budurwarsa ɗauke da harsashi fiye da 90 a Borno

“Laila ta hadu da wani a London. Lauyanta ya shaida cewa ta hadu da mutumin a otal ne inda yake aiki. Bayan yin bincike mai zurfi, an gano dama sun hadu da shi tun watanni 8 kafin lokacin ta yanar gizo.”

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, jun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel