Bidiyon sanatan Najeriya yayin da yake aikin sarrafa cunkoson ababen hawa a Abuja

Bidiyon sanatan Najeriya yayin da yake aikin sarrafa cunkoson ababen hawa a Abuja

  • Wani sanatan Najeriya ya shiga kanun labarai ba wai a kasancewarsa sanata ba, a wani bangare daban
  • Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya yi aikin sadaukarwa ga jama'a ta hanyar kula da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja
  • Yayin da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta suka yaba da wannan aikin na dan siyasar, wasu kuma na zarginsa da shiga abin da bai shafe shi ba

Abuja - Wani sanatan Najeriya ya canja sana’a na wasu ‘yan mintoci yayin da ya zama jami'i mai kula da zirga-zirgar ababen hawa.

Sanatan na Borno ta Kudu mai suna Mohammed Ali Ndume an dauki bidiyonsa ne yayin da yake kokarin sassauta cunkoson ababen hawa a wata babbar hanya a Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari

Sanata Ndume ya nuna karimci yayin da yake gudanar da aikin sarrafa zirga-zirgar ababen inda yake sanye da babbar riga.

Sanata Muhammad Ali Ndume
Martanin 'yan Najeriya yayin da sanata ke sarrafa zirga-zirgan ababen hawa a Abuja | Hoto:@insta9jablog
Asali: Instagram

A cikin wani dan gajeren bidiyo da Instablog9ja ya yada a Instagram, an ga dan siyasar yana ba da umarni ga masu ababen hawa kamar wani kwararren jami'in kula da ababen hawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani bangare na hanyar, wani mutum ya taimaka masa wanda shi ma yake sarrafa zirga-zirgar daga wani gefen.

Ba a dai san inda Sanatan ya dosa ba a lokacin da ya tsaya don kula da cunkoson ababen hawa amma abin da ya nuna cunkoson ya ragu na tsawon mintunan da ya tsaya aikin.

Martanin 'yan Najeriya

@onismate ya ce:

“Zabe ya kusa.. Nan ba da jimawa ba za mu ga Amaechi yana cin kifi da boli a Rumukoro, Natasha Akpoti na soya ayaba a mahadar Lokoja da Osibanjo na gasa masara a Pansheke ilat Abeokuta."

Kara karanta wannan

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

@nkemji yace:

"Wannan mutumin da ke tuka honda accord da alamu yana da tsare-tsare na ture Sanata."

@chu6x ya rubuta:

"Su ma zauna mana…. 2023 ta kusa yanzu…. Wasu Gwamnonin ma har sun fara cin masarar gefen hanya kamar yadda suka saba."

@cactusjonathan ya ce:

"Duk wani dan Najeriya da ya zabi wani daga cikin mutanen nan a 2023, ba zai ji dadi ba na tsawon lokaci, ku yi kokarin samun pvc dinku."

@iteegoigbo tunani:

"Ni dan Igbo ne, amma zan shaida cewa ALI yana cikin 'yan majalisar dattawan da ke aikinsu kai tsaye, ba ya riya."

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

A wani labarin, gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci sojojin da suka samu raunuka a wani kazamin fada tsakaninsu 'yan ta'adddan ISWAP a garin Rann da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru a yankin Kala Balge a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Zulum ya zanta da kuma jajanta wa dukkan sojojin da abin ya shafa a lokacin da ya ziyarce su a asibitin sojoji da ke Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Ya samu tarba daga babban kwamandan runduna ta 7 na rundunar soji, Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel