Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

  • Fitaccen mawaki Naziru Sarkin waka ya tayar da kura saboda wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram mai suna @Sarkin_wakan_san_kano
  • Ya fara wallafar ne a ranar Litinin, 6 ga watan Disamba inda ya wallafa hoton fallen Al’Kur’ani mai girma ya zagaye ayar da ta umarci a duki mata
  • A cewar mawakin, ga ayar da ta ce ayi duka, yana bukatar mabiyansa su nuna masa wacce ta ke kada a duki mata, yau kuwa har dogon bidiyo ya yi yana karin bayani

Fitaccen mawaki Nazir Sarkin waka ya janyo cece-kuce sakamakon wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram.

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce
Naziru Sarkin Waka ya yi magana kan matsayin dukan mata, lamarin ya janyo cece-kuce. Hoto: @Sarkin_wakan_san_kano
Asali: Instagram

A ranar Litinin da yamma ne mawakin ya dauki hoton wani falle na wata aya daga cikin Al’Qur’an mai girma wacce ya yi tsokaci a karkashin hoton inda yace:

Kara karanta wannan

'Ɗan iskan' ajinmu a sakandare ya zama matuƙin jirgin sama, mu masu kamun kai kuma har yau ba mu da komai

“Toh, ni dai naga ayar da tace mutum ya daki matarsa idan taci tura... Sai dai a taya ni nemo wacce tace kar a daki mata...nagode.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan wallafar ta sa mutane da dama suka dinga tsokaci suna sukarsa wasu na cewa alama ce da ke nuna yana dukan nashi matan.

Duk da hakan akwai wadanda su ka dinga goyon bayansa su na cewa umarnin Allah ne. Akwai wadanda suke ganin ba haka ya kamata ya bayyana ba, kila ya yi wa ayar wata irin fahimta ta daban.

A yau kuma ya kara yin wani dogon bidiyo wanda yace haka ayar take kuma yana nan a kan bakarsa.

Ya kara da cewa yana da matar da su ka kai shekaru 8 tare amma ko sasanta su ba a taba yi ba. Don haka ba ya nufin a yi duka, kawai yadda ayar ta zo ne ya fassara ta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ƙasaitattun Kayan Alatu Da Matashi Ya Saka a Gidansa Na Kasa, Ciki Har Da AC, Babban TV Da Kujeru

Ya hori maza da su guji dukan matansu saboda ba hallaya ta kwarai bane sannan mata su kasance masu bin dokokin mazajensu don gudun dukan.

A karkashin wallafar ya samu fiye da tsokaci dubu daya daga mutane daban-daban wadanda da dama su ka dinga sukar wannan fahimtar tasa.

Ga wasu daga cikin abubuwan da mutane suka ce game da batun:

Wata teenash_food_and_catering ta ce:

To tunda kace sai kayi addu’a a fara da yaranka in sunyi ba dadi. Mu dai iyayen ‘yan mata muna neman tsari da mijin da zai da ke mu ko ya daki yaranmu.”

hajarahabib ta ce:

“Akaramakallah ai idan ka fadi haka sai ka fadi tafsirin “wadribuhunna” din yadda a shari’ance aka umarta ayi bugun kadan ba wanda zai bar wani tabo ko ya illatar da matan.”

abu.khadeejah1 kuwa cewa ya yi:

“Allah ta raba mu da jahilci.”

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

Kara karanta wannan

Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel