Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

  • Babbar mota ta samu matsalar birki, inda ya murkushe wasu kananan yara a wani yankin jihar Legas
  • A rahotannin da muke samu, an ce direban ya guda, amma an kamo shi an mika shi ga 'yan sandan yankin
  • Matasa sun tada hankali, inda suka yi yunkurin kutsawa ofishin 'yan sanda don su kwato shi su illata shi

Legas - Akalla yara ‘yan makaranta 13 ne suka mutu a Legas a ranar Talata bayan da wata motar dakon kaya ta samu matsalar birki ta bi ta kansu, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Yaran suna dawowa daga makaranta ne lokacin da lamarin ya faru, Premium Times ta ruwaito.

Kawo yanzu dai ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Taswirar jihar Legas
Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta | Hoto: researchgate.net

Hadarin ya afku ne a kan titin Isheri, daf da ofishin ‘yan sanda na Ojodu yayin da yaran suka taso daga makaranta, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shaidu sun ce direban babbar motan ya banke yaran ne daf kusa da makarantar Ojodu Grammar School sannan ya gudu.

A cewar wani shaida:

“An bi shi aka kama shi a kusa da Ogba sannan aka dawo da shi caji ofis. Don haka ne matasa suka kai hari ofishin ‘yan sanda.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, fusatattun matasa sun lalata manyan motoci a kewayen yankin tare da jifa da duwatsu a cikin ofishin ‘yan sanda.

Hakazalika, jami’an ‘yan sanda sun tare kofarsu suna harbin bindiga da barkonon tsohuwa don korar matasan.

Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin

A wani labarin, Ibrahim Jubril, daya daga cikin iyayen da aka tsinci gawar ‘ya’yansu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a Legas, ya magantu kan wannan mummunan lamari.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Idan za a iya tunawa, an tsinci gawarwakin yara takwas da aka ce ‘yan shekara hudu zuwa shida ne a cikin wata mota da aka ajiye a kan titin Adelayo, Jah-Michael, a yankin Badagry a Legas, a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel