Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Afka Etekwuru, Sun Kashe Mutum 2 Sun Lalata Dukiyoyin Miliyoyin Naira

Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Afka Etekwuru, Sun Kashe Mutum 2 Sun Lalata Dukiyoyin Miliyoyin Naira

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari garin Etekwuru da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema na jihar Imo a safiyar yau Laraba
  • Yayin harin, sun bindige mutane biyu sun kuma raunata wasu da dama tare da lalata dukiyoyin naira
  • Eze Kenneth Okereke, Sarkin Etekwuru ya tabbatar da harin ya kuma yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro su kawo musu dauki

Imo - A kalla mutane biyu ne wasu yan bindiga suka halaka a garin Etekwuru da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema na jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindigan sun kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin naira yayin harin da suka kai a safiyar ranar Laraba.

Baya ga lalata kadarori na miliyoyin naira, maharan sun kuma raunta wasu daga cikin mazauna garin kafin su tafi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Afka Etekwuru, Sun Kashe Mutum 2 Sun Lalata Dukiyoyin Miliyoyin Naira
TaswirarJihar Imo. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kawo yanzu ba a san dalilin da yasa maharan suka afkawa garin ba, amma wakilin Daily Trust ya rahoto cewa lamarin ya bar mutanen garin cikin tashin hankali.

Sarki Garin Etekwuru ya tabbatar da kai harin

Sarkin garin, Eze Kenneth Okereke, ya tabbatar da afkuwar harin yana mai kira ga jami'an tsaro su kawo wa mutanensa dauki.

Wannan ba shine karo na farko da ake kawo irin wannan harin ba.

A ranar 21 ga watan Oktoba, wasu yan bindiga sun kona fada da motar sarkin garin yayin da suka kai hari gidansa da nufin su halaka shi.

An dade ana kai wa gari hari

Harin da aka kai fadar sarkin na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu yan daba da dakarun sojoji sun yi arangama a garin.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna

Sarkin ya rubuta wasika zuwa ga gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yana fada masa halin da ya ke ciki na cewa ya yi hijira daga garin yana kuma neman taimako.

Mun Kashe Hakimi Don Yana Bincikar Shugaban Mu: Ɗan Ta'adda Da Suka Kashe Hakimin Ƴantumaki a Katsina

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a Jihar Katsina ta sanar da kama daya daga cikin 'yan bindigan da suka kai hari tare da kashe hakimin 'Yantumaki, Abubakar Atiku, da mai tsaronsa, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan yayin da ya ke holen wanda ake zargin tare da wasu, a ranar Talata a Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta rahoto yadda 'yan bindiga suka kashe hakimin a ranar 1 ga watan Yunin 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel