Da Dum-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna

Da Dum-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna

  • Wasu yan bindiga sun sake kai sabon hari ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutane
  • Daya daga cikin waɗan da suka yi yunkurin sace wa kuma ya kubuta, yace maharan sun tasa keyar mata da kananan yara akalla 36
  • Wannan harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu mahara sun kashe mutum 2, sun kuma sace wasu 50 a kudancin Kaduna

Kaduna - Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu tsagerun yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari ƙauyukan karamar hukumar Birnin Gwari, dake jihar Kaduna.

Rahotannin da muka samu sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da sama da mutum 36 zuwa wani ɓoyayyen wuri a cikin jeji.

Yan bindigan sun kai waɗan nan hare-haren ne a ranar Lahadi da kuma safiyar ranar Litinin da suka gabata.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Jihar Kaduna
Da Dum-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin mutanen da maharan suka yi kokarin sacewa ya kuɓuta, Malam Muhammad, ya tabbatar da cewa maharan sun tasa keyar mata, kananan yara da sauran su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan na zuwa bayan wasu tsagerun yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai makamancin irin wannan hari a Kudancin Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun hallaka mutum biyu, sannan kuma suka yi awon gaba da wasu mutane kimanin 50 yayin harin.

Matasan yankin sun maida martani

Matasan kudancin Kaduna, karakashin kungiyar su SOKAPU, sun bayyana tsantsar takaicin su da faruwar wannan lamarin.

Bugu da ƙari matasan sun yi kira ga al'ummarsu musamman matasa da su tashi su kare kansu daga ta'addancin waɗan nan mutanen.

A cewar matasan ta bakin shugaban matasa na kungiyar SOKAPU, lokaci ya yi da zasu tashi tsaye, su ɗauki mataki ba wai su zuba ido ana ɗai-ɗaita yankin su ba.

Kara karanta wannan

Matasan jihar Kaduna sun fusata, Sun aike da kakkausan sako ga miyagun yan bindiga

A wani labarin na daban kuma Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama-bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja

Rahoto ya bayyana cewa yayin harin, jirgin sojojin saman ya sheke yan bindiga akalla 45 sannan kuma ya lalata ma'adanar makaman su.

Yan bindigan na amfani da wannan wurin a matsayin maɓoyarsu, da kuma kaddamar da hari kan matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel