Mun Kashe Hakimi Don Yana Bincikar Shugaban Mu: Ɗan Ta'adda Da Suka Kashe Hakimin Ƴantumaki a Katsina

Mun Kashe Hakimi Don Yana Bincikar Shugaban Mu: Ɗan Ta'adda Da Suka Kashe Hakimin Ƴantumaki a Katsina

  • Yan sanda a jihar Katsina sun damke wani dan bindiga da ake zargi yana cikin wadanda suka kai hari fadar Hakimin Yantumaki, suka halaka shi
  • Wanda ake zargin, Yusuf Abubakar, ya amsa cewa shi da wasu 'yan tawagarsa su hudu ne suka kashe hakimin saboda yana bincikar shugabansu
  • Abubakar ya ce sauran 'yan tawagar su da suka aikata laifin tare suna can a daji a yayin da yan sandan suka ce ana cigaba da fadada bincike a kan lamarin

Katsina - Rundunar 'yan sanda a Jihar Katsina ta sanar da kama daya daga cikin 'yan bindigan da suka kai hari tare da kashe hakimin 'Yantumaki, Abubakar Atiku, da mai tsaronsa, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan yayin da ya ke holen wanda ake zargin tare da wasu, a ranar Talata a Katsina.

'Yan sanda sun kama mutumin da ake zargin ya kashe hakimi a Katsina
An kama daya daga cikin wadanda suka kashe Hakimin Yantumaki a Katsina. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta rahoto yadda 'yan bindiga suka kashe hakimin a ranar 1 ga watan Yunin 2020

SP Gambo Isah ya ce:

"A ranar 3 ga watan Disambar 2021, Yan sanda sun yi nasarar kama wani dan shekara 20, Yusuf Abdullahi dan kauyen Kagara, Karamar hukumar Matazu, da ake zargin yana tawagar yan bindigan da suka kai hari gidan marigayi hakimin Yantumaki, Alhaji Abubakar Atiku.
"An bindige Atiku, mai shekaru 55 tare da mai tsaronsa marigayi Gambo Isah.
"A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wadanda suka aikata laifin. A cewarsa, shi da wasu yan bindigan hudu, da yanzu suke daji suka aikata laifin.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa har yanzu ana cigaba da bincike a kan lamarin kamar yadda ya zo a ruwayar Premium Times.

Mun kashe shi ne don yana bincikar shugaban mu

Wanda ake zargin ya amsa cewa sune suka kashe hakimin saboda yana binciken shugabansu

"Ina cikin wadanda suka kashe hakimin. Mun kashe shi saboda ya gane daya daga cikinmu kuma yana kokarin ganin an kama Shamsu. Ya san Shamsu kuma ya san dan fashi ne.
"Mun gano cewa yana kokarin kama Shamsu ya mika ga hannun yan sanda don haka muka kashe shi.
"Shamsu ne ya bindige shi da kansa da muka tafi fadarsa yayin da mu kuma muka cigaba da harbi don tada yamutsi a gari. Mun kuma kashe mai gadinsa," in ji shi.

Ya ce sunan sauran yan tawagar nasu, Kabir, Salmanu shi kansa da kuma Shamsu.

Sauran ukun suna can daji sun boye.

Rashin Tausayi: Yadda 'yan bindiga suka kona fasinjoji 10 da ransu da tsakar rana a Sokoto

A wani rahoton, 'yan fashin daji sun babbaka wasu ‘yan gudun hijira a kauyen Gidan Bawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto da ransu, Daily Trust ta ruwaito.

An samu rahoto akan yadda suke hanyarsu ta zuwa Gadab Gayan da ke jihar Kaduna don zarcewa kudancin Najeriya su ci gaba da rayuwa.

Daily Trust ta bayyana yadda su ke cikin abin hawarsu ‘yan bindigan su ka yi musu zobe tare da bude musu wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel