Sau 7 ina yin warwas a UTME, mahaifina ya rasu, Budurwa ta bada labarinta mai taba zuciya da kayan NYSC

Sau 7 ina yin warwas a UTME, mahaifina ya rasu, Budurwa ta bada labarinta mai taba zuciya da kayan NYSC

  • Jama'a na ta aikawa da sakon taya murna ga wata budurwar Najeriya bayan ta tafi wajabtacciyar hidimar kasar ta duk da kalubalen da ta fuskanta
  • A yayin shagalin murnar wannan nasarar da ta samu a rayuwa, ta bayar da labarin ta mai taba zuciya bayan kammala karatun sakandaren ta a shekarar 2009
  • Kamar yadda ta ce, ta rubuta jarabawar shiga jami'a har sau bakwai kafin ta samu gurbin karatu a 2016 kuma a wannan halin mahaifin ta ya rasu

Wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita yanar gizo da labarin rayuwarta mai matukar taba zuciya bayan ta wallafa murnar ta ta tafiya hidimar kasa.

A yayin wallafa hotunanta inda ta ke sanye da khakin NYSC, @Teeecookie ta rubuta cewa ta kammala karatun sakandare a shekarar 2009 amma ta dinga bajewa a jarabawar UTME.

Kara karanta wannan

Matar aure ta yiwa budurwar mijinta wanka da fetur sannan ta banka mata wuta har lahira

Sau 7 ina yin warwas a UTME, mahaifina ya rasu, Budurwa ta ada labarinta mai taba zuciya da kayan NYSC
Sau 7 ina yin warwas a UTME, mahaifina ya rasu, Budurwa ta ada labarinta mai taba zuciya da kayan NYSC. Hoto daga @Teeecookie
Asali: Twitter

Sabuwar mai digirin ta ce ta yi jarabawar UTME sau bakwai kafin daga bisani ta samu makin da ake bukata domin samun gurbin karatu a jami'a a shekarar 2016.

Sai dai cike da abun tausayi, mahaifin ta ya rasu yayin da ta ke kokarin samun gurbin karatun a jami'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba ta ji da sauki ba yayin da ta ke karatu a jami'ar

'Yar bautar kasar ta bayyana cewa, ba a nan gumurzun ya kare ba, ta fara wahala wurin samun kudin makaranta amma daga bisani ta samu.

Sakamakon annobar korona da ta gallabi duniya, budurwar ta kara shekara daya a makaranta amma ta kammala da digiri mai daraja ta biyu.

Kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Twitter:

"Na kammala karatun sakandare a shekaru 12 da suka gabata. JAMB ta wahalar da ni na tsawon shekaru bakwai. A tsakanin wannan lokacin, mahaifina ya rasu. Na samu gurbin karatu a shekarar 2016.

Kara karanta wannan

Budurwar da aka kora daga jami'a a 2016, ta kammala digiri a wata jami'a, ta samu kyautuka

"Kokarin biyan kudin makaranta wani abu ne na daban. Annobar korona ta kara min shekara 1. Ban taba maimaita kwas ba tun daga aji daya har zuwa aji hudu. Daga bisani na kammala karatu da digiri mai daraja ta biyu. Ga ni nan."

'Yan Najeriya sun yi martani

@major_1118 yace:

"Ni ma a shekarar 2016 na samu gurbin karatu amma har yanzu ga mu a jami'ar. Babu karin shekarar amma yajin aiki ya saka mu gaba.

@Ayoja0 yace:

"Ina taya ki murna kan wannan nasarar. Ina fatan rayuwa ta yi miki sauki daga nan. Sarauniya."

@EkundayosamE tsokaci yayi da cewa:

"Na taya ki murna gaskiya, sannu a hankali za a isa inda za a kai. Ubangiji ya cigaba da yalwata murmushin fuskar ki."

@Count_Euro kuwa cewa yayi:

"Muna taya ki murna kuma muna miki fatan samun karin nasarori a nan gaba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel