Budurwar da aka kora daga jami'a a 2016, ta kammala digiri a wata jami'a, ta samu kyautuka

Budurwar da aka kora daga jami'a a 2016, ta kammala digiri a wata jami'a, ta samu kyautuka

  • Wata budurwar Najeriya ta yi murna da nasarar da ta samu a karatun ta a kafar sada zumunta inda ta bayar da labarinta
  • An kori Ibukunoluwa Areo daga jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a shekarar 2016 sakamakon rashin kokarin ta
  • Bayan shekarun da ta dauka ta na kokarin shiga makaranta, ta samu ta shiga kuma ta kammala digirin ta inda ta zama zakaran gwajin dafi har da kyautar N400k

Ibukunoluwa Areo ta kafa tarihin da wuya a goge shi a jami'ar Bowen, Iwo ta kammala digiri da sakamako mai daraja ta farko bayan kuma lambobin yabo da kyautar kudi tsaba harN400k da ta samu.

Hazikar budurwar ta wallafa labarin ta a kafafen sada zumunta inda ta hada da kyawawan hotunanta na shagalin kammala karatun ta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

Budurwar da aka kora daga jami'a a 2016, ta kammala digiri a wata jami'a, ta samu kyautuka
Budurwar da aka kora daga jami'a a 2016, ta kammala digiri a wata jami'a, ta samu kyautuka. Hoto daga LinkedIn/Ibukunoluwa Areo
Asali: UGC

Shekarun kunci

Ibukunoluwa ta wallafa labarin ta LinkedIn inda ta ce ta sha matukar wuya kafin ta samu nasara kuma ba kowa ya san hakan ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda tace, an kore ta daga jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a 2016 sakamakon rashin hazaka da ta nuna.

Kamar wannan kaddarar ba ta isa ba, ta kasa samun gurbin karatu a jami'a na tsawon shekaru biyu cif saboda shirmen da ta yi wuri cike fom da kuma rashin makin da ya dace.

Ta dage inda daga bisani ta nemi gurbin karatu a jami'ar Bowen da ke Iwo inda aka bata aji biyu kuma ta samu nasara.

Nasarorin da ta samu a jami'ar

Ibukunoluwa ta ce ta samu nasarori kamar haka:

  1. Ta kammala digiri a fannin tattalin arziki
  2. Ta kammala a matsayin dalibar da ta fi kowa kwazo a sashen karatunsu
  3. Ta kammala a matsayin dalibar da ta fi kowa kwazo a jami'ar.

Kara karanta wannan

Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu, za a biya ta diyyar miliyoyi

Bayan shekara 5 an kore shi daga jami'a, ya koma inda ya samu digiri mai daraja ta 1 da lambobin yabo

A wani labari na daban, duk rintsi da tsanani tare da kalubalen da ya fuskanta a baya, wani matashi dan Najeriya ya nuna cewa zai iya inda ya kammala digirinsa.

Timilehin P. Abayomi ya ce an kore shi daga jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife bayan ya kwashe shekaru biyar ya na karatu.

A wallafar murna da yayi a LinkedIn, Timilehin bai sanar da dalilin da yasa aka kore shi ba amma ya ce hakan ya matukar gigita shi kuma mahaifiyar shi ta dinga kuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel