Babbar Magana: 'Yan sanda sun runtuma kame a Abuja, sun harbi jami'in DSS

Babbar Magana: 'Yan sanda sun runtuma kame a Abuja, sun harbi jami'in DSS

  • Jami'an 'yan sanda a Abuja sun harbi wani jami'in DSS yayin da suka kai farmaki kan wasu al'ummomi a birnin Abuja
  • A rahoton da muka samo, an ce jami'an na DSS na kan hanyar tafiya ne lokacin da 'yan sanda suka kai farmaki yankin
  • Hakazalika, an kame mutane da yawa, inda majiya tace duk wanda aka kama sai da ya biya N5000 a matsayin beli

Abuja - Jami’an ‘yan sanda daga sashin Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, sun runtuma kame a unguwar Dakwa da ke Abuja, inda suka harbe wani jami’in hukumar DSS.

Jami’in na DSS da ba a gano waye shi ba an ce yana kan hanyar wucewa ne a lokacin da aka harbe shi a kamen na Dakwa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matafiya da dama sun makale a yayin da ‘yan bindiga suka tare hanya a Neja

Akalla mutane 37 ne da wasu masu wucewa ta yankin aka kama a yayin samamen da aka gudanar da misalin karfe 8 na dare.

'Yan sandan Najeriya
Babbar Magana: 'Yan sanda sun runtuma kame a Abuja, sun harbi jami'in DSS | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin, Aliyu Ibrahim, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai gadi a daya daga cikin makarantu masu zaman kansu da ke yankin, yana daya daga cikin wadanda aka kama aka kai su ofishin ‘yan sanda inda suka kwana.

Ya ce sauran mutanen da aka kama sun hada da ‘yan kasuwa, masu shayi da masu nama da kuma masu tuka baburan kasuwa.

A cewarsa:

“Sun afkawa unguwar ne da motoci uku da suka hada da motar Hilux, bas da kuma wata motar daukar kaya.
"Sun yi aiki ne tare da 'yan bangan yankin da suka hau baburan da aka kama, yayin da aka kai masu su da sauran mutanen da aka kama a cikin motocin 'yan sanda."

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa an saki mutanen da aka kama ne da safiyar washegarin kama su bayan biyan belin N5,000 kowannensu.

Da yake mayar da martani, jami’in ‘yan sanda na yankin Zuba, CSP Osor Moses, ya tabbatar da harbin jami’in DSS, sai dai ya ce yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada.

Sai dai ya mika wakilin majiyarmu ga rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja domin jin karin bayani kan lamarin.

A rundunar ‘yan sandan ta babban birnin tarayya, kakakin ‘yan sandan, DSP Josephine Adeh, ta ce za ta yi bayani ga manema labarai amma ba ta yi ba har lokacin hada rahoton, inji SarahaReporters..

'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue

Wasu 'yan bindiga sun bindige wani babban malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Benue da ke Ugbokolo a yammacin jiya Lahadi a sashin Eke na hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Okkwu na jihar Benue.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace basarake da matarsa da mutane da dama a Katsina

Marigayin malamin, mai suna Adah Echobu Chris, wanda aka fi sani da, “The Bull”, an yi zargin wasu ‘yan bindiga ne suka kai masa hari a lokacin da yake komawa mazauninsa da ke Ugbokolo daga garin Eke, da ke yankin karkara.

Shaidu sun ce malamin yana tuka motarsa ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kama shi suka harbe shi har lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel