Innalillahi: An tura yara zuwa Islamiyya, an tsinci gawarwakinsu a cikin wata mota

Innalillahi: An tura yara zuwa Islamiyya, an tsinci gawarwakinsu a cikin wata mota

  • An tsinci gawarwakin wasu yara 8 da suke wasa a cikin wata mota a jihar Legas, lamarin da ya tada hankalin iyaye sosai
  • An kai gawarwakin dakin ajiyar gawarwaki a wani asibiti a Badagry ta jihar domin ci gaba da binciko musabbabin mutuwarsu
  • An rahoto cewa, wasu daga cikin yaran an tura su makarantar Islamiyya ne, amma ba a ga dawowarsu ba sai aka gano gawarwaki

Legas - An tsinci gawarwakin wasu yara takwas a cikin wata mota da aka ajiye akan titin Adelayo, Jah-Micheal a Badagry ta jihar Legas.

An ce yaran suna tsakanin shekaru hudu zuwa shida, inji rahoton TheCable.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 4 ga watan Disamba.

Taswirar jihar Legas
Innalillahi: An tura yara Islamiyya, an tsinci gawarwakin 8 a cikin wata mota | Hoto: researchgate.net

Adekunle Ajisebutu, kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Shaidanun aljanu sun kwace titunan Bauchi, jami'in FRSC ya ce za a fara yakarsu

Ajisebutu ya ce:

"Yaran takwas an ce sun kulle kansu ne cikin wata motar da aka yasar a lokacin da suke wasa.
“An gano gawarwakinsu kuma an ajiye su a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry domin a tantance ainihin musabbabin mutuwarsu."

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma ce kwamishinan ‘yan sanda a Legas, Hakeem Odumosu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan al’amuran da suka shafi mutuwarsu.

Odumosu ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa, hudu daga cikin yaran ‘yan gida daya ne da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya.

Wani mazaunin yankin mai suna Taiwo ya shaida cewa yaran sun je makarantar Arabiyya ranar Asabar da lokacin dawowarsu yayi kuma iyayensu ba su gan su ba sai hankali ya tashi, suka fara nema, inda aka gano gawarwakinsu daga baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano

A wani labarin, an sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar a unguwar Kawaji da ke Kano a ranar Asabar.

Masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da ita a cikin babur din dai-daita sahu yayin da suka yaudare ta da sunan rage hanya.

Daily Nigerian ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da karfe 5 na yamma lokacin da yarinyar da sauran yaran unguwar suke dawowa daga makarantar islamiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel