Wata sabuwa: Shaidanun aljanu sun kwace titunan Bauchi, jami'in FRSC ya ce za a fara yakarsu

Wata sabuwa: Shaidanun aljanu sun kwace titunan Bauchi, jami'in FRSC ya ce za a fara yakarsu

  • A kalla mutane 35 ne suka mutu a wasu hadurran motoci daban-daban a fadin jihar Bauchi a cikin watan Nuwamba
  • Wani babban jami'in hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar ya ce yana zargin hadurran na da alaka da shaidanun aljanu
  • Yusuf Abdullahi, kwamandan sashen rundunar FRSC a jihar ta Arewa maso Gabas ya ce shaidanun aljanu sun kama hanyoyin jihar

Bauchi - Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) dake Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya koka kan yadda ake samun yawaitar hadurran mota a jihar a cikin watan Nuwamba.

Ya ce a cikin watan da ya gabata, mutane a kalla 35 ne suka mutu a wasu hadurran mota a fadin jihar.

Motocin hukumar FRSC
Shaidanun aljanu sun kwace titunan Bauchi, jami'in FRSC ya ce za su fara yakarsu | Hoto: dailynigerian.com

Kwamandan sashin da yake bayyana damuwarsa kan lamarin ya ci gaba da bayyana cewa:

“Shaidanun aljanu sun mamaye hanyoyin Bauchi a ‘yan kwanakin nan.”

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa Abdullahi, wanda ke jawabi ga mambobin kungiyar na musamman a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba ya ce:

“Ina baku hakurin fada muku, amma gaskiyar magana ita ce shaidanun ajnau sun mamaye hanyoyinmu a jihar Bauchi. Lallai muna bukatar mu tashi tsaye mu yi wani abu don kwato hanyoyin.
“Al’amarin ya yi muni sosai, a cikin watan Nuwamba; lamari ne da ake samun mace-mace a kowace rana domin ba a kasa samun mutuwar mutane 35 ba sakamakon hadurra a fadin jihar. Wannan abin damuwa ne kuma abin tada hankali, dole ne a yi wani abu da sauri."

Vanguard ya ruwaito shji inda yake bayyana yadda aka samu haddura a kan wasu titunan.

A cewarsa:

“A kan hanyar Bauchi zuwa Kano, mun samu hadurran da suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 15. Wata Keke NAPEP ta yi hadari ita kadai kafin wata mota Sharon da ke zuwa ta ta bi kansa.

Kara karanta wannan

'Yan banga sun jawo 'yan bindiga sun hallaka mazauna a Sokoto, gwamnati ta fusata

“A kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos, wasu motoci sun uo karo da manyan motocin tafiye-tafiye da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15 tare da kone wasu daga cikinsu kurmus."

Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

A wani labarin na daban, wani direban babban mota da ba a san ko wanene ba ya kashe jami'in hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, a kan babban titin Hotoro ring - road a jihar Kano, Vanguard ta ruwaito.

An gano cewa lamarin ya faru ne a yayin da jami'in na FRSC ya yi yunkurin bincika babbar motan.

Wani shaidan ganin ido mai suna Abubakar Abubakar ya ce an turo jami'in ne ya fado kasa a yayin da ya ke duba motar kamar yadda Nigerian Tracker ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel