Matasan jihar Kaduna sun fusata, Sun aike da kakkausan sako ga miyagun yan bindiga

Matasan jihar Kaduna sun fusata, Sun aike da kakkausan sako ga miyagun yan bindiga

  • Matasan Kudancin jihar Kaduna sun bayyana cewa lokaci ya yi da zasu tashi tsaye wajen kare yankunan su daga ta'addanci
  • Matasan yankin karkashin kungiyar mutanen kudancin Kaduna, SOKAPU, sun sha alwashin kare kan su da yankinsu daga ta'addancin yan bindiga
  • A harin baya-bayan nan, wasu yan bindiga sun hallaka mutun biyu, sannan suka sace wasu kimamin 50 a yankin Unguwan Gimbiya

Kaduna - Matasan kudancin Kaduna sun sha alwashin cewa ba zasu sake naɗe hannu suna kallo yan bindiga na kai hari yankunansu, suna sace mutane ba.

Matasan sun gargaɗi yan bindigan ne karkashin kungiyar mutanen kudancin Kaduna (SOKAPU) bangaren matasa, kamar yadda Vamguard ta rahoto.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban matasan SOKAPU na ƙasa, Kwamaret John Isaac, ya fitar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan wata 1 hannun yan bindiga, an saki Kiristoci masu bauta 60 da aka sace a Coci

Jihar Kaduna
Matasan jihar Kaduna sun fusata, Sun aike da kakkausan sako ga miyagun yan bindiga Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Matasan sun yi kira ga mutanen dake zaune a yankin kudancin Kaduna su tashi tsaye su daina jiran kowa, su kare kansu daga sharrin waɗan nan mutanen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matasan suka ce:

"Wajibi mu tashi tsaye domin kare kan mu daga sharrin yan ta'addan nan, waɗan da suka samu mafaka a dazukan mu."

Bamu ji daɗin sace sama da mutum 50 ba - Matasan SOKAPU

Matasan sun kuma bayyana rashin jin daɗinsu da dana sani kan harin da yan ta'addan suka kashe mutum biyu. kuma suka tasa keyar wasu 50 a Ungwan Gimbiya, Sabon Tasha dake karamar hukumar Chikun.

Kazalika matasan sun bayyana cewa a watan Yuli, wasu maharan sun farmaki waɗan nan yankuna.

Tribune Online ta rahoto matasan na cewa:

"A harin watan Yuli, an kashe mana mutum ɗaya, kuma mun biya miliyoyin kudi a matsayin fansa."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

"A kwanan nan kuma sun kashe mutum biyu, sun sace wasu adadi mai yawa a Unguwan Gimbiya, Sabon Tasha, kuma garin yana cikin birnin Kaduna."

Matasan SOKAPU sun kara da cewa abun da takaici yadda yan ta'adda ke ɗai-ɗaita kauyuka, kuma ya zama wajibi abun ya zo ƙarshe.

A wani labarin na daban kuma ministan Buhari ya bayyana babban dalilin da yasa gwamnatin tarayya ke jan kafa wajen fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci

Ministan shari'a yace gwamnati na bin komai daki-daki, kuma zata tabbatar ta yi komai a lokacin da ya dace.

Minsitan ya kuma tabbatar da cewa wannan gwamnatin ba zata kyale ko waye ta gano yana da hannu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel