Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

  • DPO na yan sandan Furgar ya samu yanci bayan kwashe kwanaki shida hannun masu garkuwa da mutane
  • Yan bindigan sun tare shi a hanya a watan Nuwamba yayinda dogarinsa ya gudu
  • Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kira iyalinsa kuma sun bukaci kudin fansa milyan hamsin

Babban jami'in dan sanda kuma DPO na garin Fugar, karamar hukumar Etsako Central a jihar Edo, CSP Ibrahim Ishaq, ya shaki kamshin yanci bayan kimanin mako guda hannun yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa an saki DPOn ne da daren Alhamis, 2 ga Disamba, 2021.

Kakakin yan sandan jihar Edo, Bello Kongtons, ya tabbatar da sakin DPOn amma bai yi tsokaci kan ko an biya kudin fansa ba.

Yace:

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

"Ina mai tabbatar da cewa jami'an tsaro sun ceto DPO na Fugar daga hannun yan bindiga."

Yan bindiga sun sake DPO
Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu Hoto: Sahara Reporters
Asali: Facebook

A baya mun kawo muku cewa DPO na ofishin Fugar dake jihar Edo, CSP Ibrahim Aliyu Ishaq, yayi arangama da tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Edo.

PRNigeria ta ruwaito cewa yan bindigan sun yi awon gaba da shi ne kusa Rafin Ise dake tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode ranar Juma'a.

Rahoton ya kara da cewa tuni sun tuntubi iyalansa kan maganar kudin fansansa.

Gabanin komarwa Edo, CSO Ishaq yayi DPO a ofishin yan sandan Dakata a jihar Kano.

A riwayar Solacebase, yan bindiga sun bukaci kudi N50m kafin su sake shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel