Dalibin SS3 ya doki Malami har lahira saboda ya zane kanwarsa

Dalibin SS3 ya doki Malami har lahira saboda ya zane kanwarsa

  • Ana neman dalibin SS3 ruwa a jallo bayan kashe Malamin makaranta saboda an zane 'yar uwarsa
  • Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa an tsare kanwar amma Matashin ya gudu ba'a gansa ba
  • Mutane da dama sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan lamari

Wani dalibin ajin karshe a makarantar Sakandare mai suna Micheal Ogbeise ya lallasa Malaminsa, Ezuego Joseph, har lahira a jihar Delta, don an zane masa kanwa.

Wannan abu ya auku ne a wani makaranta mai zaman kanta a Abraka, jihar Delta, rahoton Tribune.

Malamin ya ladabdatar da dalibarsa ne mai suna Promise, wacce kanwace ga Micheal.

Kawai sai Micheal wanda bai ji dadin hakan ya garzaya wajen Malamin ya fara naushinsa sai da ya daina numfashi.

Dalibin SS3 ya doki Malami har lahira saboda ya zane kanwarsa
Dalibin SS3 ya doki Malami har lahira saboda ya zane kanwarsa Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

Kakakin yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, wannan ya tabbatar da labarin ya bayyana cewa yana ya gudu kuma ana nemana ruwa a jallo.

Yace:

"Labarin gaskiya ne. Dalibin ya kaiwa Malamin hari kuma ya yanke jiki ya fadi. Yarinyar na hannun hukuma, amma yayanta, wanda yayi kisan, ya arce."
"Babu ruwanmu da iyayensa, kawai shi muke son mu kama."

Kaakin yan sanda ya kara da cewa a ranar Juma'a Malamin ya kwanta dama a asibiti kuma tuni an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawwaki.

Malamin ya kasance mai karantar da dalibai Kimiyar Aikin Noma (Agric) da Kimiyar rayuwar dan Adam (Biology).

Gwamnatin jihar Legas ta rufe wata makaranta kan mutuwar ɗalibi

Gwamnatin jihar ta rufe Kwalejin Dowen ta Lekki Phase 1 don samun damar bincike akan mutuwar wani dalibi, Sylvester Oromoni Jnr, wanda ake hasashen ya mutu ne sakamakon wata kungiyar asiri a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Matashin zai auri mata biyu rana guda bayan dirka musu ciki

Rufe makarantar ya biyo bayan ziyarar da kwamishinan ilimin jihar, Mrs Folasade Adefisayo da sauran manya na ma’aikatar ilimin su ka kai makarantar ranar Juma’a.

‘Yan uwan yaron sun yi zargin ya mutu ne sakamakon raunukan da wani dalibi ya ji masa saboda tsananin duka akan kin amincewarsa da shiga wata kungiyar asiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel