Matashi zai auri mata biyu rana guda bayan ya dirka musu ciki

Matashi zai auri mata biyu rana guda bayan ya dirka musu ciki

  • Mutane a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan sabuwar katin gayyatar aure a jihar Delta
  • Wani Mutumi mai suna John Erere Nana na gab da angwancewa da mata biyu bayan dirka musu juna biyu
  • Auren wanda aka shirya ranar Asabar na shan yabo da suka bakin jama'a

Ughelli, Delta - Wani mutumi dan jihar Delta, kudancin Najeriya na gab da angwancewa da dirka-dirkan mata biyu lokaci guda.

Mutumin mai suna John Erere Nana zai auri yan matan masu suna Patience Boyi da Elohor Dudu ne bayan sun dauki juna biyu daga garesa.

Matashin zai auri mata biyu ranar guda bayan dirka musu ciki
Matashin zai auri mata biyu ranar guda bayan dirka musu ciki Hoto: Instablog9ja
Asali: Facebook

A hotunan da Instablog9ja ya daura kan Instagram, an shirya auren gargajiyan ne a makarantar Firamaren Ishere dake Oviri Agbarho, karamar hukumar Ughelli North, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

Dukkansu yan jihar Delta, sun sanya irin kaya guda a hoton dake jikin katin gayyatan.

Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu:

Comrade S.N yace:

Kai wannan ba karamin jarumi bane gaskiya ..
Bana shi zamu bawa kyautar Gwarzon Shekara a bisa wanga kokari da yayi✌

Khalid Hassan Abubakar:

Wannan shege ne, Shegantaka se Anna

Muktar Mahmud Muktar:

Lalle yayi kokari sosai

Saifullahi Sa'idu Gangara

Da an Bari sun haihu a had'a da Suna kawai

Aleeyou Habeeb Abdoulkhareem:

gwaji yayi kuma yanzu ya tabbatar da cewa ba juyoyi ze auro

Asali: Legit.ng

Online view pixel